Tafarki Zuwa Gadir KhumIdanun Fadima (A.S) suna yawo tsakanin taurari suna kallon sasannin sama inda babanta ya yi tafiyar isra’i da mi’iraji a “Kai ne mai wanzuwa, komai mai bacewa ne, taurari wata... Fararen rayuka suna fuskantar ka, ba ruwansu da kayoyin da ke A Kuba’a Jibril (A.S) ya sauka yana dauke da kalmomin sama zuwa ga mutumin da ya gudu daga uwar alkaryu (Makka) yana ba shi labarin matafiya da ’yarsa, da matar da ta rene shi, da saurayin da ya rena a dakinsa, wanda yayin da ya girma ya tsaya a gefensa yana kare shi iyakar karfinsa. A nan ne fa mafarkin nan na wahayi ya tabbata, farfajiyar Kuba’a ta yi yalwa, yayin da Annabi (S.A.W) ya gina masallacin farko a Musulunci. “Wadanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma tunani a cikin halittar sammai da kasa (suna cewa): Ya Ubangijinmu ba ka halicci wannan don wasa ba, tsarki ya tabbata gare ka, ka kiyashe mu azabar wuta. Sai Ubangijinsu ya amsa musu cewa ni ba na tozarta ladan aikin mai aiki, namiji ko mace, sashenku daga sashe yake, wadanda suka yi hijira daga gidajensu aka cutar da su a tafarkina, suka yi yaki aka kashe su, zan shafe kurakuransu, kuma in shigar da su aljanna koramu suna gudana ta karkashinta, sakamako daga wajen Allah, Allah a wajansa akwai kyakkyawan sakamakoâ€. Annabi (S.A.W) ya kasance yana sauraron isowar tawagar matafiya da ’yarsa da mai renonsa suke ciki, kuma kalmomin da Jibril (A.S) ya Annabi (S.A.W) ya tsaya yana tunanin sahara mai nisan gani yana sauraron masoyan da ya bar su a wani lokaci na dare, kurayen Makka sun kewaye shi. Dare ya mamaye sahara, Annabi (S.A.W) ya koma hayin Bani Saham, a fuskarsa akwai bakin ciki kamar bakin cikin annabi Adam ranar da yake binciken Hawwa a bayan kasa. Matafiyan (masu hijira) sun isa da aminci, Uban (S.A.W) ya tattaka domin haduwa da tarbar ’yarsa abar tunawarsa daga Hadiza (A.S), Hadizar da ta tafi ta bar shi shi kadai. ‘Yar ta rungume Babanta, ta dulmiya cikin tunaninsa, idanunta cike da hawaye, hawayen farin ciki da rahma. Mamakin girman wahalar da Muhammad ya sha! Mamakin girman wahalar da Annabawa suka sha! Ta yiwu ya ba da mamaki kwarai ga wasu mata su ga mutumin da ya haura shekara hamsin ya zama kwatankwacin misali na dan yaro a karkashin renon babarsa. Muhammad (S.A.W) ya kalli idanun ’yarsa da suka zama suna binciken saurayin da ya sayar da ransa saboda Allah a cikinsu, amsar da ke idanunta shi ne: Ga shi can ya Baba, shi ne... wanda kafafunsa suka tsattsage, jini ya zubo ta cikinsu da sukan kaya da zafin rana da wahalar sahara, ba shi da taguwa ko rakumi. Idanun Annabi (S.A.W) suka amsa cewa: Ashe dan’uwana ne take so! Sai Muhammad (S.A.W) ya tafi don haduwa da dan’uwansa mai hijira, shi kuwa saurayi ya tashi domin haduwa da Manzon sama (S.A.W) yana mai mancewa da zoginsa da wahalhalunsa. Annabi (S.A.W) ya sanya tafinsa mai kanshin Rahikul mahtum na Annabta ya shafa duga-dugan saurayi mai hijira kamar uwa tana shafa
|