JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



Hanyar kadai da za ta iya shiryar da mu kan layin da rayuwar Imam Sadik ta duka ita ce gano muhimman alamu na rayuwar Imam ta hanyar ka’idoji, a game, na salon tunanin Imam da dabi’unsa. Kana mu yi bincike kan abubuwan tarihi da suka danganci wannan rayuwa da hujjojin tarihi da suke warwatse da kuma irin wadancan abubuwa masu dangantaka da rayuwar Imam wadanda ba na tarihi ba har mu kai ga rarrabewar al’amarin filla-filla.

ALAMOMI A RAYUWAR IMAM SADIK (A.S).

Muhimman alamomi wadanda suke fitattu a rayuwar Imam Sadik (a.s)  idan muka lura da mahangar bahasinmu, suna iya tattaruwa cikin wadannan:-

1. Bayyana sha’anin imamanci da kira zuwa gare shi.

2. Sharhi kan hukunce-hukunce da tafsirin Alkur’ani dai-dai da abin da mazhabin Ahlulbaiti ya gada daga Manzon Allah (s.a.w.a)

  3. kafa tsari na sirri kan manufa da kuma siyasa.

Hanyar da bahasinmu zai dauka ita ce yin bincike kan kowani daya daga wadannan alamomi sannan daga karshe mu sanya wani jadawalin ayyukan Imam (a.s)  Duk wannan zai kasance da salon masu tarihi ba na masu hadisi ba, gwargwadon iyawarmu.

1. Bayyana sha’anin imamanci da kuma yin kira zuwa gare shi.

Wannan maudu’i yana daukar masayin mafi bayyanan alamomin kiran imaman Ahlulbaiti (a.s) tun shekarun farko bayan kaurar Annabin rahama (s.a.w.a). Mas’alar tabbatar da imamancin Ahlulbaiti ita ce al’amari na kan gaba wajen kira a dukkan zamunnan imamanci. Muna iya ganin wannan mas’alar a yunkurin Imam Hussain ibn Ali (a.s)  da kuma yunkurin ‘ya‘yan imaman Ahlulbaiti kamar Zaid ibn Ali. Kirar Imam Sadik ita ma ba ta fita daga wanna fagen ba.

Kafin mu bijiro da hujjoji kan wannan maudu’i ya zama wajibi  tukun mu fara da bayanin ma’anar (imama) ‘imamanci’ a tunanin musulunci. Kuma mene  ne kira zuwa ga imamanci?  Kalmar imamanci a asalinta tana nufin jagoranci sake ba kaidi. A tunanin musulunci kuwa galibi ana amfani da ita ne a kebance. Wannan  wurin kuwa shi ne jagoranci a sha’anin halin zaman jama’a walau wajen tsarin tunani ne ko kuwa tsarin siyasa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next