JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).



A wata riwaya daga Imam Sadik (a.s) akwai ta’kidi kan biyayya ga ‘wasiyyai’.  Riwayar ta fayyace cewa wasiyyan su ne wadanda Alkur’ani ya kira da lakabin ulul amri .[6]

Daruruwan riwayoyi da ke rarrabe cikin babi daban-daban suna fayyace mana cewa manufar imam da imamanci a tunanin shi’a ba komai ba ce face jagoranci da gudanarwa na al’amuran musulmar al’umma kuma imaman Ahlulabaiti (a.s) basu  takaita wajen da’awar imamanci kan abin da ya shafi  tunani da ma’nawiyya kadai ba, a’a suna kira da cewa hukuma ita ma tasu ce. Kiransu mai fadi kamar haka mai kuma tattara dukkan sassa hakika kira ce ta wata harakar siyasa da kuma soji wadda take da zimmar karbar shugabanci.

Wannan batu ya ci gaba da zama boyayye ga masu bincike a zamunnan da suka biyo baya amma a fahimtar sahabban imamai da wadanda suka yi zamani da su batun yana daga mafi bayyanannun al’amura. A cikin daya daga kasidunsa na Hashimiyyat, Kumait yana sifanta imaman Ahlulbaiti da cewa su ne shugabanni masu jagorantar mutane ta wata hanya wacce ta saba gaba daya da hanyar da azzaluman mahukunta suka bi, inda suke mu’amala da mutane tamkar dabbobi.[7]

Mu koma ga maudu’in asali cewa kashin baya a kiran Imam Sadik (a.s) da sauran imaman Ahlulbaiti (a.s) shi ne batun imamanci. A tare da mu akwai riwayoyi masu karfafa juna wadanda suke tabbatar da wannan batu na tarihi. Ana nakalto su a bayyane tare kuma da wannan fayyacewa daga Imam Sadik (a.s) inda ya yi da’awar imamanci. Za mu bayyana  nan gaba cewa lokacin da Imam yake bayar da sanarwar wannan kiran  nasa, yana ganin kansa cikin wani mataki na jihadi mai bukatar ya yi watsi da mahukuntan zamaninsa, ta hanya bayyananna kuma kai tsaye, sannan kuma ya sanar cewa shi ne ma’abocin hakki na hakika, ma’abocin shugabanci (wilaya) da kuma imamanci. Irin wannan fitowa, bisa al’ada, tana nufin an ketare sauran matakan jihadi wadanda suke gabatarta tare da nasara. Dole ne ya kasance farkawa a siyasance da yanayin zaman jama’a ta zama tuni ta sami goyon baya mai fadi, ana jin shirin mutane ya yi karfi a ko wani wuri, shimfida kan manufa ta kankama ga wani adadin mutane mai dama, sannan jama’a masu yawa sun yi imani da wajibcin kafa hukumar gaskiya da adalci, sannan daga  karshe, jagoran ya zama ya riga ya dauki kuduri mai karfi akan wannan fito-na-fito mai tsanani. Idan wadannan sharuddan basu cika ba,sanarda imamancin wani mutum ayyananne da jagorancin sa na gaskiya  ga al’umma abu ne mai tattare da ujula ba kuma cimma manufa tare da shi.

Wata mas’alar da ba makawa ga karfafawa game da ita a wannan bayanin ita ce, a wadansu lokutan Imam Sadik (a.s) ba ya takaita kan tabbatar da imamancinsa kadai, yana ma ambaton sunayen imaman gaskiya magabatansa tare da ambaton nasa sunan, watau, bisa hakika, yana gabatar da silsilar imaman Ahlulbaiti tare da sadarwa, daya bayan daya, ta yanda yayyankewa ko rarrabewa ba ya yiwu wa.

Wannna matsayin yana nuni da dangantakar da ke akwai tsakanin jihadin imaman Ahlulbaiti (a.s) da dorewarsa tun daga zamunnan da suka gabata har zuwa lokacin Imam Sadik (a.s). Imam Sadik (a.s) yana bada sanarwar imamancinsa a matsayin shi na wani sakamakon  da ba makawa zai biyo bayan imamancin magabatansa, kuma da wannan yake bayyana tushen wanna kiran da zurfin kafuwarta  a tarihin sakon musulunci, da dangantakarta da ma’abocin kiran, Manzon mai girma, mafificin tsira da aminci ya tabbata gare shi. Bari mu kawo wasu samfurin kiran Imam:-

Riwayar Amru ibn Abi Mikdam ita ce  mafi ban-sha’awa a wannan babin, tana kuma sauwara wani yanayi mai ban mamaki.

A ranar tara ga watan Zulhijja, yayin da mahajjata suka taru a Arfa domin tsayuwa gashi sun riga sun hallara a wannan wuri daga ko ina: kamar daga karshen kasar Kurasan har zuwa gabar tekun Atlantika,  a wannan wuri mai hadarin gaske, inda kira a cikinsa tana iya aika amon ta zuwa nisan duniyar musulunci. Imam ya hadu da wannan taron jama’u masu yawa saboda ya isar musu da kalmarsa. Mai ruwaya yace:- na ga Imam ya tsaya cikin jama’an nan, ya daga murya da kyau domin ya isa kunnuwar mahalarta sannan daga bisani ya kai ga kunnuwan  talikai, yana kira kamar haka:-“Ya ku mutane ! Lallai Manzon Allah ya kasance shi ne shugaba (imam), sannan Ali ibn Abi Talib, sannan Hassan, sannan Hussaini, sannan Ali ibn Hussain, sannan Muhammad Ibn Ali, sannan ……..” Yana wannan kiran sau uku ga wadanda suke gabansa, da gefensa na dama, da gefensa na hagu da kuma bayansa, kira goma-sha biyu ke nan”[8]

A wata riwayar daga Abu Sabah Alkinani cewa Imam Sadik (a.s) ya sifanta kansa da kuma imaman shi’a da cewa ganima (anfal) da zababben dukiya tasu ce.

Daga Abi Sabah ya ce:- Abu Abdillah ( a.s) ya ce da ni: “Ya Aba Sabah, mu mutane ne wadanda Allah ya farlanta biyayya gare mu. Ganima tamu ce, zababben dukiya namu ne, mu ne matabbata cikin sani kuma mu ne wadanda aka yi wa hasada wadannan da Allah ya fade su cikin littafinsa”[9]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 next