JOGARANCIN IMAM SADIK (A.S).Imami ko kuma shugaban siyasa a al’ummar musulunci dole ne ya zama abin nadawa daga Allah ta hanyar sanarwa daga Annabi. Dole ne ya zama jagora a tsarin tunani, mai fasssarar Alkur’ani , masanin dukkan mas’alolin addini masu zurfi da rikitarwa (daka’ik)da kuma alamu irin na ramzi a cikin addini. Wajibi ne ya zama ma’asumi wanda aka kubutar daga duk wani aibi na halitta ko dabi’u ko aibin da taliki yake janyo wa kansa. Wajibi ne ya zama ya fito ne daga tsatso mai tsarki da tsabta. Saboda wannan a fahimtar musulunci na karnin farko da na biyu imamanci na dauke da ma’anar jagorancin siyasa, a fahimtar mabiya Ahlulbaiti a kebe kuwa, kalmar tana hadawa da ma’anar jagorancin tsarin tunani da dabi’u, baicin siyasa. Shi’a tana karbar imamancin mutum yayin da ya mallaki wadansu sifofi; baicin karfin gudanar da al’amuran zamantakewan jama’a, ya wajaba ya zama zai iya fuskantarwa da shiryarwa da ilmantarwa a fagagen tunani da addini, da tsarkake dabi’u da halaye. Idan kuwa ba shi da karfin aikata wannan to ba zai yiwu ya hau matakin “imamanci na gaskiya†ba. A ra’ayin shi’a kyan gudanarwa a siyasance da karfin kula da mas’alar soji da yaki da makamantansu, sifofin da suka zama isashshen ma’auni wajen wadanda ba shi’a ba, a ganin shi’a wadannan ba su isa ba. Saboda haka manufar imamanci wajen mabiya Ahlulbaiti tana komawa ga yanda imami ko shugaban al’umma yake bayar da misalin jagorancin al’umma ta hanyar rayuwarsa cikin jama’a da kuma yanda yake hulda da dai-daikun mutane. Imami shi ne madugu a tafiyar, shi yake koyarwa da tarbiyyantarwa kuma shi ne jagoran gudanar da rayuwa. Idan mun lura da wannan to Annabi (s.a.w.a) shi ma imam ne saboda shi ne jagoran tunani da siyasa na al’ummar da ya kafa ginshikanta. Bayan Annabi, al’umma tana bukatar wani imami ya gaje shi ya dauki kayan nauye-nauyen da suka rataya a wuyarsa, a cikinsu kuwa akwai nauyi na siyasa. Shi’a suna imani da cewa Annabi ya yi furuci da nassi kan halifancin Ali ibn Abi Talib (a.s) sannan imamanci ya ci gaba a bayansa, zuwa ma’asuman imamai a zuriyarsa. Ya zama wajibi mu yi ishara da cewa shiga junan nauye-nauyen nan uku na imamanci watau jagorancin siyasa da koyar da addini da tarbiyyar dabi’u da ruhi wadanda musulunci ya sifantu da su, sun samo asali ne daga rashin rabewa tsakanin wadannan sassa uku a shirin da musulunci ya tanadar wa rayuwar bil Adama. Jagorancin al’umma dole ne ya hada da jagorantarta a wadannan fagage uku. Saboda wannan fadi da halin tattarau na manufar imamanci a wajen shi’a, ba makawa nadin imami ya zama daga Allah subhanahu wa ta’ala. Muna iya tsamowa daga abin da ya gabata cewa imamanci, sabanin yanda ma’abota biri-bokon ra’ayi suke gani, ba manufa ce wacce ake kwatantawa da ‘halifanci’ ko ‘hukuma’ ko wani matsayi wanda ya takaita da al’amuran ma’anawiyya da ruhi da tunani ba, a’a, shi, a tunanin shi’a, jagorancin al’umma ne a al’amuran addininta da abinda ya danganci hakan kamar tsara rayuwa a yanayin zaman jama’a da na siyasa ( shugaban kasa). Kazalika imamanci shi ne kula da sha’anin koyarwa da shiryarwa da kuma fuskantarwa a al’amuran wa’anawiyya da ruhi da warware matsalolin tunani da manufar (aidiyolojiyya) musulunci (jagorancin tunani). Abin takaici, wannan bayyanannar mas’ala ta zama bakuwa a zakatan mafiya yawan masu akidar imamanci. Domin haka muna ganin ya zama dole mu kawo wasu misalai daga daruruwan hujjoji na Alkur’ani da hadisi a kan wannan. A cikin littafin (babi) Alhujja na Alkafi akwai wani hadisi wanda aka ruwaito daga Imam Ali ibn Musa Alrida(a.s) ya ambaci abin da ya danganci sanin imam da sifofinsa, filla-filla, bayanin da ya kunshi ma’anoni masu zurfi da gwanin kyau. Daga wadannan riwayoyi akwai wadanda suka bayyana imamanci da cewa: “Shi matsayin anabawa ne, gadon wasiyyai. Sannan dai imamanci halifancin Allah ne kuma halifancin Manzo ne,mukamin Amirul muminina (a.s) ne, gadon Hassan da Hussaini (a.s)ne. Sannan kuma imamanci ragamar addini ne,dadaiton musulmi ne, kyautatuwan duniya ne, daukakar muminai ne. Shi imamanci ginshikin musulunci ne mai yado da albarka, reshensa ne mai daukaka. Da imami ne salla da zakka da azumi da haji da jihadi suke cika, da shi ne ake samar da ganima ( fai’i) da sadakoki da zartar da haddodi da hukunce-hukunce da kare iyakokin kasaâ€[3] A kan imami kuma cewa ya yi:- “(Shi) tauraruwa mai shiryarwa ne, ruwan dadi ne, matsera daga halaka ne, girgije mai kawo ruwa ne, mafakar bayi a lokacin bala’i ne, amintaccen Allah kan halitarsa ne, hujjarsa bisa bayinsa ne, halifansa a kasashe ne, mai kira zuwa ga Allah, mai tsare hurumin Allah ne, daidaiton addini ne, daukakar musulmi ne, fushin munafukai ne, kuma halakan kafirai neâ€[4]
|