Alamomin Soyayya Don Allah385. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: wanda ya riki wani dan’uwa a musulunci to Allah zai gina masa babban (dogon) gini a aljanna daga al’jauhar[16]. 386. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Hakika masoya ana ganin dakunansu a aljanna kamar tauraro mai bollowa daga gabas ko yamma, sai a ce: su waye wadannan? Sai a ce: wadannan su ne masu so saboda Allah madaukaki[17]. 387. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: masoya saboda Allah a ranar kiyama suna kan wata kasa ta zabarjade kore a wata inuwar al’arshinsa daga damarsa -kuma dukkan hannayensa dama ne- fuskokinsu suna mafi tsananin fari, kuma mafi haske daga rana mai bullowa, dukkan wani mala’ika makusanci ko Annabi mursali yana burinsu a matsayinsu, mutane suna cewa: su waye wadannan? Sai a ce: wadannan su ne masu soyayya saboda Allah [18]. 388. Amali daga Abdullahi dan mas’ud: Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: masu soyayya saboda Allah madaukaki suna kan wasu duraku na jan yakutu a aljanna, suna kallon mutanen aljanna, sai idan dayansu ya leko kansa sai kyawunsa ya cika gidajen ‘yan aljanna, sai ‘yan aljanna su ce: ku fito mu kalli masu soyayya saboda Allah madaukaki. Ya ce: sai su futo su gan su, kowane dayansu fuskarsa kamar wata a daren cikarsa, a kan goshinsu: (an rubuta) wadannan su ne masu soyayya saboda Allah[19]. 3 / 11 Rigo Zuwa Aljanna
389. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: masu soyayya saboda Allah madaukaki su ne farkon wadanda zasu zo tafki (alkausara) a ranar kiyama[20]. |
back | 1 2 3 4 5 | next |