Alamomin Soyayya Don Allah



Hadisi:

380. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Ya kai Anas ka yawaita abokai, hakika su sashensu masu ceton juna ne ga sashe[11].

3 / 7

Amincin Ranar Kiyama

381. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: masu soyayya saboda Allah suna cikin inuwar al’arshin Allah ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa, mutane suna firgita su ba sa firgita, kuma mutane suna tsorata su ba sa tsorata[12].

3 / 8

Haramcin Wuta

382. Daga Imam Muhammad Bakir (S.A.W) ya ce: yayin da Allah ya yi wa Musa dan imrana (A.S) magana, sai Musa (A.S) ya ce: … Ubangijina, mene ne sakamakon wanda ya so masu bin ka saboda sonka? Sai ya ce: ya kai Musa (A.S), zan haramta masa wuta[13].

3 / 9

Shiga Aljanna Babu Hisabi

383. Daga littafin Kafi, daga abu Hamza assumali, Daga Imam Zainul abidin (A.S) ya ce: idan Allah ya tara mutanen farko da na karshe sai mai shela ya yi shela da mutane zasu ji, sai ya ce; ina masu so saboda Allah ? Sai wasu jama’ar mutane su tashi, sai a ce musu: ku tafi zuwa aljanna babu wani hisabi. Sai ya ce: sai mala’iku su hadu da su. Sai su ce: zuwa ina? Sai su ce: zuwa aljanna babu wani hisabi. Sai ya ce: sai su ce: ku wane irin mutane ne? sai su ce: mu ne masu soyayya saboda Allah. Ya ce: sai su ce: mene ne ayyukanku? sai su ce: mun kasance muna so saboda Allah ne, kuma muna ki saboda Allah ne. ya ce: sai su ce: madalla da ladan masu aiki[14].

3 / 10

Darajoji A Cikin Aljanna

384. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: wanda ya yi ‘yan’uwantaka saboda Allah to Allah zai daukaka masa daraja a aljanna da wani abu da aikinsa ba zai iya samu ba[15].



back 1 2 3 4 5 next