Alamomin Soyayya Don Allah



Alamomin Soyayya Saboda Allah

Hujjatul Islam Muhammad Raishahari

Hafiz Muhammad Sa’id Kano

Fasali na uku: Alamomin Soyayya Saboda Allah (S.W.T)

3 / 1

Kamalar Imani

372. Daga Imam Hasan Askari (A.S) daga iyayensa (A.S): ya ce: wata rana Manzon Allah (S.A.W) ya ce; da wani daga sahabbansa: Ya kai Abdullah! ka yi so saboda Allah, kuma ka yi ki saboda Allah, kuma ka yi kauna saboda Allah, kuma ka yi gaba saboda Allah, ka sani ba a samun yardar Allah sai da hakan, kuma mutum ba zai samu dandanon imani ba –komai yawan sallarsa da azuminsa- har sai ya kasance kamar haka. Hakika a yau ‘yan’uwantakarku da mutane a wannan zamanin mafi yawa ta kasance saboda duniya ne, a kan haka ne suke soyayya kuma a kanta ne suke kiyayya, kuma hakan ba zai amfana musu komai ba daga Allah (S.W.T). sai wani mutum ya ce: ya ma’aikin Allah, yaya zan san cewa; na yi soyayya saboda Allah kuma na yi kiyayya saboda Allah ? kuma waye masoyin Allah har sai in so shi, kuma waye makiyin Allah har sai in ki shi? Sai Manzon Allah (S.A.W) ya yi masa nuni zuwa ga Ali (A.S), sai ya ce: shin kana ganin wannan ?! Sai ya ce: E. Sai ya ce: wannan ne masoyin Allah; sai ka so shi, kuma makiyin wannan makiyin Allah ne; sai ka ki shi, kuma ka so masoyin wannan koda kuwa shi ne makashin babanka da danka, ka kuma ki makiyin wannan koda kuwa babanka ne ko kuma danka[1].

373. Daga Imam Ja’afar Sadik (S.A.W) ya ce: wanda ya so domin Allah kuma ya ki domin Allah kuma ya bayar domin Allah, to wannan yana daga wadanda imaninsa ya kammala[2].

3 / 2

Yanke tasiri n Shedan

374. Daga Imam Muhammad Bakir (S.A.W) ya ce: na umarce ku da so saboda Allah da kuma kauna da taimako a kan aiki nagari; domin hakan yana kange su; sarki azzalumi da shedan[3].

3 / 3

Ikhlasin Soyayya

375. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: a kan soyayya saboda Allah ne soyayya take tsarkaka[4].

376. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: wanda abotakarsa ta kasance saboda Allah to abotakarsa zata kasance girmama, kuma kaunarsa ta kasance madaidaiciya[5].

3 / 4



1 2 3 4 5 next