Hada Salloli Biyu



Al’amari Na Shida: Sabawar Mash’huriyar Maganar Sauran Mazhabobi Ga Abin da Ya Zo Karara A Ingantattun Littattafai

A wannan fakara zamu yi nuni zuwa ga ruwayoyi da suka zo a sihah, kuma suka yi bayanin mas’alar halarcin hadawa tsakanin salloli biyu koda babu wani uzuri, wanda wannan ya sabawa ra’ayi mash’huri na mazhabobin ahlussunna:

1- Sihah sun kawo cewa Manzon Allah (S.A.W) ya hada tsakanin salloli biyu a zaman gida ba tare da wani uzuri ba, kamar yadda Sahihul buhari[33] ya kawo, da sahihul Muslim[34] da sunan Abu Dawud[35] da sunan Tirmizi[36] da sunan Nisa’i[37] da Muwadda Maliku[38] da sunan Darukudni[39] da Mu’ujamul kabir na Tabarani[40] da Kanzul Ummal[41].

Kuma wannan ruwayoyi sun ambaci cewa manzon Allah (S.A.W) ya hada salloli biyu ba tare da wani uzuri ba[42].

Mun samu a ruwayar Dan Abbas a lokacin da yake nakalto mana duka nau’o’in biyu daga ruwayoyi wato hadawa ba tare da wani uzuri ba, wanda ya fahimci rashin wani sababi na daban daga aikin Annabi (S.A.W) kuma Abu huraira ya karfafi wannan aiki na Dan Abbas yayin da aka tambaye shi.

Sannan Dan Abbas ya yi kaico ga mutumin da ya yi masa musun jinkirta sallar magariba daga farkon lokacinta, da kuma hada wa tsakanin salloli biyu babu wani uzuri da fadinsa: Kaiconka! mu zaka gaya wa Sunna? Mun kasance muna hadawa a lokacin Manzo (S.A.W)[43].

2- Sannan ruwayoyin sun yi nuni da hadawa sake-ba-kaidi, kamar fadinsa: “Manzo ya yi mana sallar azahar da la’asar, magariba da issha ba tare da wani tsoro ko safara ba”[44].

Kuma Manzo ya yi sallar azahar da la’asar a hade a Madina ba tare da tsoro ko safara ba, Zubair ya ce: Sai na tambayi Sa’id saboda me? Sai ya ce na tambayi Dan Abbas kamar yadda ka tambaye ni sai ya ce: Yana gudun kada al’ummarsa ta wahala[45].

A yakin Tabuka ya yi jam’i tsakanin azahar da la’asar da kuma magariba da issha, sai na ce: Me ya sa ya yi haka? Sai ya ce: “Yana gudun kada al’ummarsa ta wahala”[46]. Kuma ya hada ba tare da ruwan sama ba[47],  kuma ya hada sallar azahar da la’asar da magariba da issha ba tare da cewa akwai tsoro ko ruwan sama ba[48], da hadisin na yi salla a bayan manzo (S.A.W) takwas gaba da ya da kuma bakwai gaba daya[49], wadannan ruwayoyi dukkansu suna nuna rashin kebancewa da lokutan uzuri.

Na’am akwai ruwaya daya da Tirmizi ya rawaito da ta saraya ta fuskacin sanadi, daga Abu Salama Yahaya dan Khalaf Al’basari: Mu’utamar dan Sulaiman ya ba mu labari daga babansa daga Hanash, daga Ikrama, daga Dan Abbas, daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Wanda ya hada salla biyu ba wani uzuri ya zo wa kofa daga kofofin zunubai”.

Abu Isa da Hanash suka ce: Wannan Abu Ali Arrahabiyyi shi ne Husaini dan Kais kuma shi rarrauna ne gun ma’abota hadisi, Ahmad da waninsa sun raunata shi[50]. Buhari ya ce: Hadisinsa duka karya ne kuma ba a rubuta hadisinsa. Akili ya ce: Wannan hadisi na wanda ya hada salla ba uzuri ya zo wa kofa daga kofofin bata ba a la’akari da shi, ba a san kowa ba sai shi, kuma ba shi da asali, domin ya inganta daga Dan Abbas cewa: Annabi (S.A.W) ya hada sallolin azahar da la’asar[51], saboda haka wannan ruwaya ba ta da wani kebancewa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next