Hada Salloli Biyu



Kuma wannan makaranta ta iya tarbiyyatar da mutane da suke shirye domin kamfata daga wannan ilmi kuma ta fitar wa al’umma manyan malamai masu biyayya ga tafarkin Ahlul baiti (A.S), suna masu gamewa da sanin dukkan mas’alolin mazhabobi daban-daban, da kuma akidoji a cikin da’irar musulunci da wajanta, suna masu bayar da mafi kyawon amsa da bayanai a tsawonn zamanin da ya gabata.

Hakika majma Ahlul baiti (A.S) ya gaggauta yana mai farawa daga nauyin da yake kansa da ya dauka a kafadunsa domin kariya ga sakon musulunci wanda ma’abota mazhabobi da kuma masu akidu da suka saba wa musulunci suka damfaru da su, yana mai bin tafarkin Ahlul Baiti (A.S) da mabiyansu da suka kwadaitar da raddi kan kalu-balen wannan zamani da kuma kokarin dawwama a kan tafarkin gwagwarmaya daidai gwargwadon abin da kowane zamani yake bukata.

Ilimin da littattafan malamai masana ma’abota bin koyarwar Ahlul baiti (A.S) suka taskace shi a wannan al’amari ba shi da misali, domin shi madogara ce ta ilmi da yake karfafa da dogara da hankali da hujja, yake kuma nisantar son rai da zargi, yake kuma magana da malamai masu tunani daga ma’abota kwarewa, maganar da hankali yake yarda da ita kuma dabi’ar dan Adam kubutacciya take karbar ta.

Kokarin majma ya zo ne domin ganin an gabatar wa dalibai sabuwar marhalar wannan ilimi mai wadata a shafin tattaunawa da tambaya da kuma raddin shubuha da a kan tayar daga lokaci zuwa lokaci tsawon zamani, ko kuma ake kawo wa a yau musamman ma da taimakon wasu kungiyoyi masu kin musulunci da musulmi a cikin sarkar sama ta intanet da makamantansu, muna masu nisantar abin da yake maras kyau, muna masu kwadayin motsa tunanin masu hankali da masu neman gaskiya domin su bude idanunsu a kan gaskiyar da koyarwar da Ahlul baiti (A.S) suka gabatar wa duniya baki daya a zamanin da hankula suke cika, alakar mutane da tunani take samuwa cikin gaggawa.

Ba makawa mu yi nuni da cewa wannan tattararrun bahasosi an tanade su ne a lujna ta musamman da Hujjatul Islam Abul Fadal Islami yake shugabanta tare da wasu manya da suka hada da Sayyid Munzir Hakim, da Shaikh Abudlkarim Bahabahani, da Sayyid Abdurrahim Musawi, da Shaikh Abdul Amir Assuldani, da Shaikh Muhammadul Amini, da Shaikh Muhammad Hashimi Al’amili, da Sayyid Muhammad Rida aali Ayyub, da Shaikh Ali Baharami, da Husaini Salihi, da Aziz Al’ukabi.

Kuma muna mika godiya mai yawa ga dukkan wadanan da kuma ma’abota falala da bincike da suka hada da: Shaikh Yusuf Garawi, da Shaikh Ja’afarul Hadi, da Ustaz Sa’ib Abdulhamid, domin bibiyar da kowannensu ya yi wa wadannan bahasosi da kuma bayanansu masu kima.

Fatanmu shi ne ya zama mun gabatar da abin da zamu iya na kokarin sauke nauyin da yake kanmu game da wannan sako mai girma na ubangijinmu da ya aiko manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya domin ya daukaka shi a kan dukkan wani addini kuma Allah ya isa shaida.

Majma Ahlul baiti (A.S)
Qom

Hada Salloli Biyu

Gabatarwa

Mazhabobin musulunci gaba daya sun hadu a kan halarcin hada sallar azahar da la’asar a lokaci guda, da kuma tsakanin sallar magariba da issha a lokaci daya, amma an yi sabani a kan dalla-dallan wannan Magana ta fuskacin sharudda da dalilan da zasu sa haka, daga ciki akwai wanda ya tafi a kan cewa ya halarta a Arfa da Muzdalifa, daga ciki akwai wanda ya kara da lokacin safara, da dai sauransu.

Amma abin takaici shi ne sai ga wasu suna tuhumar makarantar Ahlul baiti (A.S) da cewa sun saba wa shari’a, saboda kawai su sun yi hukunci da cewa hada salloli biyu ba uzuri ma ya halatta, alhalin dalilin shari’a a gun jama’a biyu (Sunna da Shi’a) suna karfafa halarcin kamar yadda zamu gani.

Don haka ne zamu yi bincike game da wannan mas’ala gun wadanda ba mabiya Ahlul baiti (A.S) ba, da kuma dalilan shari’a da suka dogara da ita mu ga hakikanin asalinta daga asalin shari’a, sannan sai mu yi la’akari da matsayin Ahlul baiti (A.S) kan wannan mas’ala cikin wadannan bayanai masu zuwa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next