Hada Salloli Biyu



1- Ya kasance a ranar Arfa.

2- Ya kasance mai harama da hajji.

3- Ya yi salla bayan limami.

4- Sallar azahar ta kasance ingantacciya, idan ta bace to dole ne a sake ta, a nan kuma bai halatta ba ya hada ta tare da la’asar, sai dai ya yi sallar la’asar idan lokacinta ya shiga.

Na biyu: Ya halatta a yi jam’i a magariba da issha jam’in jinkirtawa da sharadi biyu:

Ya zama a Muzdalifa.

Ya zama mai harama da hajji[10].

Amma Ibn Taimiyya ya amsa yayin da aka tambaye shi game da wannan mas’ala sai ya ce: Ya halatta hada wa ga tabo mai tsanani da iska mai tsanani mai sanyi a dare mai duhu da makamantan wannan koda babu ruwan sama mai saukowa a mafi ingancin maganganun malamai, wanna shi ya fi su yi salla a gidajensu, domin barin hadawa a masallaci da yin salla a cikin gida bidi’a ce da ta sabawa Sunna, domin Sunna shi ne ya yi salla biyar a masallaci, sallar hadawa a masallaci shi ya fi salla a gidaje daidaiku da ittifakin malamai wadanda suke halatta hadawa kamar Maliku da Shafi’i da Ahmad”[11].

A wanann fakara zamu kawo bincike game da ruwayoyin da littattafai sihah suka ruwaito wacce take karfafa halarcin hada salla babu wani dalili.

Abu Na Uku: Ingantattun Littattafai Suna

Karfafa Halarcin Hadawa Kai Tsaye

1- Daga Sa’id dan Jubair daga dan Abbas ya ce: “Manzon Allah (S.A.W) ya yi sallar azahar da la’asar a hade, da magariba da issha a hade ba tare da wani tsoro ba ko tafiya”[12].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next