Hada Salloli BiyuHada Salloli Biyu

Mawallafi: Majma’al Alami Li AhlilBait (A.S)

Mafassari: Hafiz Muhammad Sa’id

“Ka tsayar da salla ga karkatar rana zuwa ga duhun dare, da kuma karatun alfijir hakika karatun alfijir ya kasance abin halarta ne”. Surar Isra: 78[1].

“Jibril (A.S) ya zo wajan Manzo Allah (S.A.W) sai ya sanar da shi lokacin salla, ya ce ka yi sallar asuba yayin da alfijir yaketo, ka yi sallar farko yayin da rana ta karkata, ka yi sallar la’asar bayanta, sallar magari idan kaskon ya buya, sallar issha idan shafaki ya buya, sai ya zo masa washegari, sai ya ce: Ka waye da safiya sai ya waye da ita, sannan sai ya jinkirta azahar yayin lokacin da ya sallaci la’asar a cikinsa, ya yi sallar la’asar bayanta, ya yi sallar magariba kafin faduwar shafaki, ya yi sallar issha yayin da sulusin dare ya tafi, sannan sai ya ce: tsakanin wadannan lokuta biyu lokaci ne”. Wasa’ilusshi’a: 3\116, H 1- 4795[2].

Gabatarwar Majma

Lallai yana daga cikin dabi’ar mutane su yi sabani a junansu, sai dai Allah yana son wannan sabanin ya takaita a cikin kewayen ingantaccen imani, saboda haka ne ba makawa ya zamanto akwai ma’auni tabbatacce da masu sabani zasu koma zuwa gare shi. Allah madaukakin sarki ya saukar da littafi da gaskiya domin ya yi hukunci tsakanin mutane da gaskiya cikin abin da suka saba a cikinsa[1].

Da babu wannan gaskiya guda daya, to da al’amarin rayuwa ba zai daidaitu ba, Wannan shi ne abin da Kur’ani yake tabbatar da shi kuma yake bisa ka’idar tauhidi, sannan sai daga baya aka samu karkata da sabani da camfe-camfe har mutane suka nisanta daga wannan asasi nisanta mai girma.

Ta haka ne ta bayyana cewa mutane ba su ne masu cancantar su yi hukunci da gaskiya ko karya ba matukar sun kasance suna iya biye wa son rai da bata da zalunci.

Duk da littafin Allah ya sauka da shiriya ya kuma isa zuwa ga mutane…. tare da hakan son rai ya rinjayi mutane nan da can, kwadayi da tsoro da bata suka nisantar da mutane ga karbar hukuncin littafi da komawa zuwa ga gaskiya da yake dawo da su zuwa gareta.

Bata shi ne ya jagoranci mutane a tsawon zamani zuwa ga sabani da shisshigi da kin Allah, Jahilci ya zama wani sababin sabani da rarraba, sai dai shi jahili ya kamata ne ya tambayi malamai kamar yadda Allah ya fada: “Ku tambayi ma’abota sani idan ba ku sani ba[2]”.

Ta haka ne ketare iyakar jahili ya kasance zalunci da shisshigi ga wannan asali wanda hankali yake amincewa da shi, kuma ma’abota hankula suke karkata zuwa gareshi, kuma lallai wannan shi ne mafi bayyanar ka’idoji da hanyoyi wadanda zasu toshe hanyar rarraba da sabani.

 Musulunci shi ne addinin Allah dawwamamme da hakikarsa ta bayyana cikin nassin littafin Allah (S.W.T) da sunnar manzonsa (S.A.W) da ba ya magana da son rai sai da wahayi. Kuma Allah da manzonsa sun sani cewa al’ummarsa zata yi sabani bayansa kamar yadda ta yi sabani a lokacin rayuwarsa, don haka ne Kur’ani mai girma ya sanya wa al’umma makoma da zasu dogara da ita bayan wafatin manzo (S.A.W) tana tafiya tare da shi taku-taku tana kuma gabatar wa al’umma abin da suka takaita ga fahimtarsa da tafsirinsa, wannan kuwa su ne; Ahlul Baiti (A.S), sun tsarkaka ne daga dukkan dauda da kuma kazanta wadanda Kur’ani ya sauka ga kakansu Mustapha (S.A.W), suna karbarsa suna karanta shi suna hankaltarsa da kiyayewa, sai Allah ya ba su abin da bai ba waninsu ba... Kamar yadda manzo ya yi wasiyya da su a matsayin makoma ta gaba daya a hadisin sakalain mash’huri, sai suka kwadaitu wajan kare shari’ar musulunci da Kur’ani mai girma daga fahimta ta kuskure da tafsiri na barna, suka saba da bayanin ma’anarsa madaukakiya, sai suka zama makoma kuma madogara ga al’ummar musulmi, suna kore shubuha suna masu karbar tambayoyi da hakuri da juriya. Bayan nan abin da suka bari mai yawa yana shaidawa da kyawon mu’amalarsu tare da masu tambayarsu da tattaunawa da su, kuma komawa garesu da zurfin amsawarsu yana nuni zuwa ga kasancewarsu makoma ta ilimi a wannan fage.

Hakika koyarwarsu ta kare abin da suka bari, kuma mabiyansu suka kwadaitu a kan kare shi daga tozarta, abin da yake nuni zuwa ga koyarwarsu da ta tattaro dukkan wasu rassa na ilimomin da suke kunshe cikin koyarwar addinin musulunci.1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next