Hukunce-hukuncen Shari'a



Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Wanda ya hadu da musulmi da fuskoki da harsuna biyu, to a Ranar Kiyama zai tashi da harsuna biyu na wuta[18]”.

Daga Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “Mafi munin mutane shi ne mai fuskoki da harsuna biyu, ya kan yabi dan’uwansa idan yana nan, amma ya kan cinye shi idan ba ya nan. Idan an ba shi (wani alheri) zai yi masa hassada, idan kuwa aka jarrabe shi, sai ya fita sha’aninsa (ya wofantar da shi)[19]”.

5 – Haramcin yanke abokantakar mumini, ko kuma gaba da shi, ko kuma cutar da shi.

Ruwaya ta zo daga hanyoyi daban-daban daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Idan mutum ya ce wa dan’uwansa mumini: tir, ya fita daga wilayarsa, idan kuma ya ce: kai makiyi na ne, dayansu ya kafirta, Allah ba zai karbi wani aiki daga muminin da ke cutar da dan’uwansa ba[20]”.

6- Hanin mummunan zato ga mumini ko kuma tuhumarsa.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Idan wani mumini ya tuhumci dan’uwansa imani(nsa) zai narke cikin zuciyarsa kamar yadda gishiri ke narkewa cikin ruwa[21]”.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Amirul Muminina (a.s) cikin wani zance nasa yana cewa: Ka bar aikin dan’uwanka a mafi kyaun yanayinsa, har sai wani abin da zai kawar da hakan ya bayyana maka, kada ka yi mummunan zato ga duk wani kalami da ya fito daga dan’uwanka, matukar za ka iya ba shi wata fassara ta alheri[22]”.


[1] . Wasa’il al-Shi’a 8:471, babi na 71, hadisi na 1.

[2] . Wasa’il al-Shi’a 8:471, babi na 71, hadisi na 3.

[3] . Wasa’il al-Shi’a 8:471, babi na 71, hadisi na 4.



back 1 2 3 4 5 6 next