Hukunce-hukuncen Shari'aDaga Hisham bn Salim yana cewa: ‘Na ji Aba Abdillah (a.s) yana cewa: “……hakan shi ne fadin Allah Madaukakin Sarki: “Ya ku wadanda suka yi imani! Don me kuke fadin abin da ba ku aikatawa? Ya girma ga zama abin kyama a wurin Allah, ku fadi abin da ba ku aikatawa[5]â€. 3 – Wajibcin fadin gaskiya wajen magana da kuma mu’amala da sauran mutane. Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Ku kasance masu kiran mutane zuwa gare mu cikin alheri ba tare da (amfani da) harsunanku ba, don a ga kokari, gaskiya da tsantsaini a gare ku[6]â€. Daga Zaid bn Ali daga Iyayensa yana cewa: Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Wanda ya fi kusanci gare ni Ranar Gobe daga cikinku, wanda kuma zai sami ceto na shi ne wanda ya fi ku gaskiya cikin magana, mai rike amana, wanda ya fi ku kyawawan dabi’u, da kuma wanda ya fi ku kusance da al’umma[7]â€. 4 – Samuwar wani adadi na wajibai na hakkoki tsakanin muminai, mun yi magana kan wasu daga cikinsu yayin da muke magana kan mu’amala ta musamman tsakanin muminai, bugu da kari kan sauran hakkoki da muka ishara da su a wajaje daban-daban. A nan bari mu yi nuni da wasu daga cikin ruwayoyi da suka yi magana kan wasu bangarori na wannan batu. Daga al-Mu’alla bn Khanis, daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: na tambaye shi: mene ne hakkin musulmi a kan musulmi? Sai ya ce: “Yana da hakkoki na wajibi guda bakwai, ba wanda ke da wani face sai yana da wani wajibi a kansa da matukar ya yi watsi da shi, to ya fita daga wilayar Allah da da’arsa, kuma ba shi da wani abu a wajen Allahâ€. Sai na ce masa: Ya Shugabana! Mene ne su? Sai ya ce: “Ya Mu’alla, ni ina tausaya maka ne saboda ina tsoron kada ka yi watsi da su ka ki kula, ka sani amma ka ki aikatawaâ€. Sai na ce: Babu wani karfi sai na Allah. Sai ya ce: “Mafi saukin cikinsu shi ne ka so masa abin da kake so ma kanka, ka ki masa abin da kake ki ma kanka. Hakki na biyu, ka nesanci abin da zai bata masa rai, ka bi yardarsa, ka bi umarninsa. Hakki na uku kuwa shi ne ka taimaka masa da kanka, dukiyarka, harshenka, hannunka da kuma kafafunka. Hakki na hudu ka kasance idanuwansa, mai masa jagora kuma madubinsa. Hakki na biyar kada ka koshi alhali shi yana jin yunwa, kada ka kashe kishirwanka alhali shi yana jin kishirwa, kada ka sanya tufafi alhali shi yana nan huntu. Hakki na shida shi ne idan har kana da mai hidima shi kuma dan’uwanka ba shi da shi, to dole ne ka tura mai maka hidimar don ya wanke masa tufafinsa, ya dafa masa abinci da gyara masa wajen kwanciya. Hakki na bakwai….., ka amsa gayyatarsa, ka tafi gaishe shi idan ba shi da lafiya, ka halarci jana’izarsa, idan har ka san yana da wata bukata, ka yi gaggawa wajen biya masa ita, ka da ka bari har ya tambaye ka, face dai ka gaggauta gaggautawa, idan har ka aikata hakan, ka sada wilayarka da wilayarsa, kuma wilayarsa da wilayaka[8]â€. Kulada Kiyaye Abubuwan Haramun
A bangaren ababen da aka haramta kuwa za mu ababe da dama da shari’a ta haramta don tabbatar da wannan nau'i na kula. 1 – Haramcin shiga gidajen mutane ba tare da izininsu ba, kai har ma da wajibcin yi musu wata ishara yayin shiga, saboda musulmi yana da wani hurumi cikin jini, dukiya, mutumci da kuma al’amurransa na musamman. Daga Abdurrahman bn Abi Abdillah yana cewa: Na tambayi Aba Abdillah (a.s) dangane da fadin Madaukakin Sarki: “Kada ku shiga gidaje wadanda ba naku ba har sai kun sami izini, kuma kun yi sallama ga ma’abutansuâ€, sai ya ce: “……….., da sallama[9]â€. Kamar yadda kuma abin da ya kamata shi ne mutum ya zauna a inda mai gidan ya zaunar da shi.
|