Hakkin HarsheHadarin harshe ya sanya shi ya kasance iyaka ce tsakanin kafirci da imani, da yin isgili da addini, ko wani abu mai tsarki na addini kamar annabi, ko littafin Allah, ko kiyayya da wasiyyan annabawa waliyyan bayin Allah, ko wani abu na tilas na larurar addini kawai, ya isa ya jefa mutum cikin kafirci ya tunkuda shi wuta. Haka nan da yin kalma daya ta imani ba tare da ayyukan alheri ba, kamar dai wanda ya musulunta a lokacin annabi (s.a.w) kuma ga shi bai taba salla ko wani aiki ba na ibada, sai kuma ya yi shahada nan take, amma wannan sai ya wajabta masa aljanna har abada. Sai dai duk da haka Allah yana karba ne idan ya kasance daga masu takawa[5], domin Fir’auna ya yi Idan mun duba wannan magana mai tsarki da daraja ta Imam Zainul-abidin (a.s), zamu ga yana cewa: “Kuma amma hakkin harshe; shi ne ka kare shi daga mummunar magana, da saba masa alheri", da mutane sun yi amfani da wannan wasiyya da an samu karancin bakin ciki a duniya, da cututtukan rai da yake da mun mutane da aka fi sani da yawan fushi ya yi karanci, sai dai dan Adam bai shirya wa kiyaye hakan ba saboda jahilcinsa da son ransa. Babban abin da ake nema daga kowane mutum a nan shi ne ya kiyaye kuma ya saba wa harshensa da fadin alheri, don haka ne duk maganar da zai yi to dole ya fara tattauna ta tukun sannan sai ya furta, idan ba haka ba kuskurensa da nadamarsa zasu yawaita. Sannan da yake cewa: "da barin maganar da ba ta da wani amfani, da kyautata wa mutane, da kyautata zance game da su, da siffanta shi da ladubba, da sanya masa takunkumi sai inda yake akwai bukata, da amfani ga duniya da addini, da kuma kame shi daga shiga dan zance mai karancin amfani, wanda ba kasafai ake kubuta daga sharrinsa ba, tare da karancin amfaninsa, kuma ya kasance bayan duban hankali da kuma dalili a kansa. Kuma adon mai hankali a cikin hankalinsa ya doru bisa kyakkyawar dabi’arsa ne a cikin harshensa", yana nuni ga cewa kamalar harshe da karanta magana ne, karancin magana yana nuna hankalin mutum ne, don haka ne ya zo a cikin hikima daga abin da Imam Ali (a.s) ya nakalto daga ma'aikin Allah (s.a.w) cewa: "Idan hankali ya cika sai magana ta yi karanci". Mizanul hikima: Muhammad RaiShahari; j 3, s 2052. Wannan magana mai daraja tana da karfafuwa da hadisai masu kima daga annabin Allah (s.a.w) da kuma ruwayoyin da Ahlul-baiti suka karbo daga gareshi. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Harshen mumini yana bayan zuciyarsa, amma zuciyar munafuki tana bayan harshensa". Nahajul-balag: Huduba, j 2, s 93. Wannan kuwa domin mumini idan ya so yin magana sai ya lura da shi, idan alheri ne sai ya fada, idan kuwa sharri ne sai ya fasa. Amma munafuki yana magana da dukkan abin da ya zo wa harshensa ne, ba ruwansa da abin da yake nasa da wanda yake kansa. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Imanin mutum ba ya daidaituwa har sai ya daidaita zuciyarsa, kuma zuciyarta ba ta daidaituwa har sai ya daidaita harshensa, duk wanda ya zai iya daga cikinku ya hadu da Allah yana mai kubutaccen hannu daga jinin musulmi da dukiyoyinsu, mai kubutaccen harshe to ya yi hakan". A'alamuddin fi sifatil Muminin: Addailami; s 106. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Wanda ya san cewa maganarsa daga iliminsa ne to zai karanta maganarsa sai dai cikin abin da yake akwai ruwansa". Nahajul-balag: Hikima 349. Mazon Allah (s.a.w) yana cewa: "Wanda ya karanta maganarsa zunubansa zasu yi karanci". Uyunul Hikam wal Mawa'iz: Ali bn Muhammad allaisi, alwasidi, s 448. Mazon Allah (s.a.w) yana cewa: "Wanda ya karanta maganarsa aibinsa zai boyu". Uyunul Hikam wal Mawa'iz: Ali bn Muhammad allaisi, alwasidi, s 455. Dogaro da wadannan koyarwa mai kima da daraja zamu ga munin hirar mutane a bakin titi, akwai mutane masu yawa a kasashenmu da suke da dakalin hira na musamman, wannan hirar da ta kasance ta karuwa ko don sadar da zumunci, ko tattauna matsaya ta ilimi, ko wata matsalar al'umma da za a warware da ta yi kyau. Amma sai ta kasance sabanin haka ne in ban da 'yan kadan daga ciki, da yawa irin wadannan wuraren suka kasance wuraren hada husuma, da yi da mutane, da gulma, da annamimanci, da karairayi.
|