Hakkin HarsheHakkin Harshe
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma amma hakkin harshe; shi ne ka kare shi daga mummunar Magana ta alfahasha -da batsa-, da saba masa alheri, da barin maganar da ba ta da wani amfani, da kyautata wa mutane, da kyautata zance game da su, da siffanta shi da ladubba, da sanya masa takunkumi sai inda yake akwai bukata, da amfani ga duniya da addini, da kuma kame shi daga shiga dan zance mai karancin amfani, wanda ba kasafai ake kubuta daga sharrinsa ba, tare da karancin amfaninsa, kuma ya kasance bayan duban hankali da kuma dalili a kansa. Kuma adon mai hankali a cikin hankalinsa ya doru bisa kyakkyawar dabi’arsa ne a cikin harshensa. Sannan babu dubara babu karfi sai da Allah". Harshe kamar yadda bayani zai zo game da sauran gabobi shi ma kamar ji da gani, da hannu, da ciki, da kafa, da farji ne, yana da hakki a kiyaye shi kamar sauran, bai halatta mu yi sabo da su ba, shari’a ta dora mana neman duniya da lahira da su ne, kuma hanyoyi ne na samu da neman Ilimi da sauran ni’imomin Allah a wannan duniya da kuma makoma. Sai mu yi amfani da gani, da ji, da tafiya, wajan neman Ilimi ko neman halal, mu ki amfani da su wurin haram. Jiki dukkaninsa yana da wadannan dokokin ne, bai halatta a zalunci wani bagare nasa ba, akwai abin da mutane da yawa sun shafa’a daga gareshi. Lalaci yana daga hanyoyin da mutane suke zaluntar kawukansu, amma da yawan mutane sun gafala da shi. Wani lokaci ana zaluntar kai ne da zaman banza har ma kana iya ganin mutum ya shantake yana ta barci wai hutawa yake yi saboda lalacewa alhali bai yi aikin komai ba. Wani kuwa yana alfahari ne da cewa babansa yana da dukiya mai yawa, sai ya zalunci kansa ba zai je ya nemi abin da zai mutunta kansa ba. Harshe shi ne mafi hadarin abu da ake iya sabo da shi ko aikata lada cikin sauki, domin amfani da shi yana da sauki, idan neman zunubi ne ya isa ka yi giba ko radar wani sai a samu zunubi mai girma, har ma wasu ruwayoyi suna cewa “Giba -yi da wani- ta fi zina muniâ€[1], amma cikin sauki a cikin wurin zama daya mutum yana iya yin giba goma. Don haka ya zama wajibi a kare shi daga maganganu munana kamar karya, da hada husuma, da giba, da annamimanci Haka nan aikin lada da alheri yake da sauki ga harshe, yin salati daya a wurin zama ya isa ya bude wasu kofofin arziki, kuma fadin magana da zata faranta wa wani rai ya isa ya samar da ladan sadaka, ya zo a ruwayoyi cewa harshe mai dadi da kalma ta alheri sadaka ne[2]. Kalma mai dadi da harshe mai hada sulhu tsakanin mutane[3] shi ne wanda Allah ya ke so, kuma shari’a ta karfafa yin hakan musamman tsakanin ma’aurata da abokan zaman tare a matsayin al’umma. Wasu mutane sun kware wajen kisan mummuke ga wasu da harsunansu saboda kiyayya imma dai mai dalili ko maras dalili, hakika na dandani dacin yi mana hassada har zuwa wannan lokaci alhalin ba mu dauki kanmu a matsayin wasu fiyayyu ba. Jafa’in wasu mutane a kanmu ya kai ga yi mana kisan mummuke da harshe, sai dai Allah yana nan a wurin hisabi. Yin kisa da harshe ta hanyar bata sunan mutane da lalata kimarsu da mutunci, da rufe ido daga kyawawansu, da yin sharri a kansu, da kuma ba wa wasu yabon aikin da suka yi wani abu ne da muka dadani dacinsa. Sai dai da zarar mun tuna da abin da aka yi wa tsarkakan bayi sai mu ga wannan ba komai ba ne don an yi wa irinmu masu laifi da zunubai wurin Allah (s.w.t). Mumini ba ya kisan mumini da harshensa, ba ya cin mutuncinsa, ba ya tona sirrinsa, mumini yana kare sirrin mumini ne a duk inda yake, yana kuma yaba masa, yana kuma toshe munanansa, yana yi masa nasiha a boye ne. Ruwaya ta zo cewa: “Mumini madubin mumini neâ€[4], idan kuwa ya kasance ke nan bai zama madubin muminai ba, to lallai ba mumini ba ne. Kisan da ake iya yi wa mutuncin mutum da harshe ya fi muni fiye da kisan da ake iya yi masa da wuka ko harsashi, da yawa wasu mutane suka cutar da wasunsu saboda hassada, ko keta da mugunta, ko don suna da sabanin akida ko na siyasa. Shia’anci yana daga cikin mazhabin da tun lokacin Manzon Allah da alayensa Ahlul-baiti (a.s) ake yi masa kisan mummuke da harsuna, wannan kuwa ya kai ga salwanta rayuka da dukiyoyi da Allah ne kawai zai yi hisabi a kai. Cikin sauki harshe yana iya shafe ladan mace na biyayyar miji, ko ya tarwatsa aure zaka samu irin wannan a al’adu yayin da wasu lokutan wasu mata sukan Harshe yana da hadarin da zai iya tarwatsa gari daya ko kasa guda, jita-jita daya takan iya fin bom din kare dangi da makamin Nukiliya hadari, sau da yawa masu kin kasashen musulmi da masu ganin hada husuma tsakanin musulmi da ‘yan’uwansu na zaman kasa daya sukan yi amfani da harshe da yada jita-jita don ganin sun kawo husuma da yaki. Kuma sau da yawa irin wannan ya faru a kasashenmu da biranenmu ya jawo kashe dubunnan mutane! mu sani babu wani abu da ya fi harshe santsi da hadari don haka sai a kiyaye shi.
|