Farisancin Shi'anci 2



Kuma idan kana son ka san sama da haka sai ka duba dukkan jagororin kabilun Larabawa da suka zo domin kawar da hukumar Umayyawa, ka koma zuwa ga littafin Ibnul Fudi marubucin tarihin Iraki na Muhammad Rida Shabibi, ya fadada tarihin daga manyan littattafai kuma ya yi sharhin hadafofin kawo wannan hari da kuma nau’in rundunonin da suka yi tarayya wajen kawo hari da dukkan wasu bayanai.

Bangare na biyu shi ne cewa rundunar da ba Larabawa ba ce ta so ne ta huce haushi da daukar fansa kan Larabawa don ba a ba ta mukamai ba a cikin hukumar Umayyawa wannan ma muna iya cewa ba ingantacce ba ne, domin da yawa daga wadanda suke ba Larabawa ba sun kama matsayoyi da mukamai masu girma a lokacin Umayyawa tun daga farko har karshe, kuma yanayin da suka samu a lokacin Abbasawa ba shi da wani bambancin azo-agani da wanda suke a kai lokacin Umayyawa, kuma Dakta Ahmad Amin ya yi nuni da hakan a cikin fadinsa: Jagorancin Farisawa ya dadu a lokacin Umayyawa musamman ma karshensa, kuma da ba su samu damar kafuwar Abbasawa ba to da sun samu wata damar daban mai wani yanayi da ya fi wancan.

Wasu jama’ar da ba Larabawa ba ne sun kama mukamai masu girma; daga cikinsu akwai Sarjun dan Mansur mai bayar da shawara ga Mu’awiya, da kuma shugaban fayel din wasiku, da shugaban haraji, da Muradis Maulan Ziyad wanda yake shugaban wasiku, da Zaza Nafrukh wanda yake jagoran harajin Iraki, da Muhammad dan Yazid maulan Ansar, wanda yake gwamnan Misira karkashin Umar dan Abdul’aziz, da Yazid dan Muslim maulan Sakif wanda yake gwamnan Misira, da kuma wasu alkalai da gwamnoni da manyan jagororin haraji, kuma sun shiga duk wani matsayi na daula da jama’arta da fadadawa.

Ta wani bangaren kuma yanayin Larabawa ba ya da wani tasiri sai daidai gwargwadon yadda zai iya tabbatar da maslahar Umayyawa ne, kuma idan suka ga ya saba da maslaharsu to sai su gwara kan Larabawa, su buga sashensu da wani sashen kamar yadda ya faru sau da yawa a lokacin jagorancin Umayyawa. Kuma Dakta Ahmad Amin ya kawo wannan yana mai sharhinsa dalla-dalla kuma yana bayyana yadda Larabawa suka rika dukan junansu; bangare-bangare sashe da sashe idan al’amarin ya kai ga hakan ne maslaha.

 

Amma Ra’ayi Na Uku:

Wannan ra’ayi yana ganin Shi’anci ya yadu ne ta hanyar Mawali (wadanda ba Larabawa ba ne) kuma suka samu martaba da kima saboda haka. To wannan ma karya ne kuma bai inganta ba, domin an kaskantar da Farisawa a lokacin Abbasawa ba sau daya ba, yana daga cikin al’amarin Abu Muslim da mabiyansa a lokacin Mansur da al’amarin Baramika lokacin Rashid, da al’amarin Ali Sahal lokacin Ma’amun da sauransu. Sai dai a dunkule cewa haka ne mawali sun yi tasiri a wasu fagagen daban, kuma an samu kutsawa da kuma tasirin Farisawa lokacin Saffah zuwa Ma’amun. Kuma wannan yana nufin babu wani tasiri da yake tabbata ga Farisawa wajen da’irar Abbasawa ta yadda zasu iya sanya su karkashinsu duk sadda suka so. Amma lokacin da Mutawakkil ya fara mulki har zuwa karshen mulkin Abbasawa to Abbasanci ya samu raunana har sai dai ya rushe, wannan kuwa ya faru ne sakamakon raunin da wannan hukuma ta samu, kuma masu rubutu sun yi bayanai masu yawa kan dalilan rushewarta.

A bisa hakika abin da ake kawowa na tasirin Mawali a cikin daular abbasiyya ya kasance kambawa ne kawai domin al’ummu ba su samu wata dama mai karfi ba a wannan lokacin sai irin wacce suke da ita a lokacin Umayyawa, kuma idan Farisawa sun samu wani tasiri da samun shiga to bai kai ga yadda zai iya kange samun shigar Larabawa ba, sai dai kawai wani samun wuri da samun shiga ne da su larabawan da kansu suka ba su saboda wasu hadafofi da suke son su cim masu. A kan haka ne ma Falhozan yake cewa: Amma batun samun shigar Farisawa da kama wurinsu kamar yadda yake, ba wani abu ba ne da za a iya tabbatar da shi ba.

Amma bangare na biyu na wannan ra’ayi na cewa Shi’anci ya samu lumfasawa lokacin Abbasawa to wannan al’amari ne da ba shi da inganci domin akasin haka ne ma ya faru, saboda Abbasawa sun cakuda hannayensu da jinin Shi'a da jagororinsu, kuma Shi’anci ya samu an kai masa hari da fadawa jarabobi masu ban tsoro a lokota mabambanta in banda wasu lokuta kamar yadda ya faru a lokacin Buwaihiyyin. A takaice dai littattafan tarihi sun kawo mana wasu irin yanayoyi masu ban tsoro da firgici na azabtarwa da ak yi wa Shi'a da neman kawarwa a lokacin Abbasawa, kuma mai karatu yana iya komawa zuwa ga kowane irin littafin tarihi manya domin ya ga wannan a fili.



back 1 2 3 4 5 6 next