Farisancin Shi'anci 2



Ra’ayi Na Farko:

Wannan ra’ayi bai inganta ba saboda cewa wadanda suka jagoranci mutane sun jagorance su ne domin kubutar da su daga zaluncin Umayyawa, kuma duk wani mai bincike yana iya duba tarihin abin da ya wakana domin sanin gaskiyar abin da ya faru na halayen hukumomin Umayyawa wanda yake cike da zalunci tun farko har zuwa faduwarsa a lokacin Marwan dan Muhammad karshen sarakunan Banu Umayya, kuma ina ganin kuskure ne ma mu kawo misali daya ko biyu a kan hakan domin dukkanin kwanakin hukuncinsu cike suke da zalunci, kuma ina neman mai karatu ya koma ya bi tarihin tun lokacin Mu’awiya na farko har zuwa karshen daular a littattafan da musulmi suka rubuta duka ba na Shi'a ba kawai. Tayiwu a ce Shi'a suna kin Umayyawa kuma suna jin haushinsu ne, amma sai ga littattafan da Dabari da Ibn Asir, da Ibn Kasir, da Ibn Khaldon, da duk abin da ka ga dama ka duba ka ga abin da suka rubuta inda al’amarin ya kai ga mawaka suna cewa:

Yakinku dai yakinku dai ya ku alayen Harbu

Ya alayen Harbu daga gareku yakinku dai

Daga gareku a cikinku zuwa gareku da ku

Akwai abin da, da mun fada da mun tozarta littattafai

 

Amma Ra’ayi Na Biyu:

Shi ma ya tabbata cewa karya ne saboda dukkan wadanda suka jagoranci yakin Larabawa ne, kuma Jahiz ya kawo hakan a cikin littafinsa mai Sunan "Manakibul atra" kuma ya ambaci jagororin yakin kamar: Kahdaba dan Shabib Atta’i, da sulaiman dan Kasir al’khuza’i, da Malik dan Haisam al’khuza’I, da Khalid dan Ibrahim az’zuhaili, da Lahzi dan Darif Almuzni, da Musa dan Ka’abul Muzni, da Kasim dan Mujashi’i Al’muzani, kamar yadda tarihi ya kawo Sunan kabilun Larabawa daban-daban wadanda suke a nan Khurasan wacce ta kasance ta haifar da mafi girma runduran da mafi yawancinsu daga Khuza’a, da Tamim, da Dayyi, da Rabi’a, da Muzaina, da wasunsu na kabilun Larabawa.



back 1 2 3 4 5 6 next