Akidojin Shi'a



Amafanin addini ga rayuwar zamantakewa: mutanen da suke rayuwa tare suna samun amfani ko cutarwa, kuma suna samun daukaka ko kaskancin duk tare.su ne ake cema al'umma.Al'umma ta gari kamar mutum daya na gari take, sannan tana da hukuncin mutum guda ne.saboda haka dole ne a samar da wasu ginshikai guda uku kafin a samu kyakkyawar al'umma wadda zata iya cin amfanin rayuwa kamar yadda ya kamata.Wadannan ginshikai kuwa su ne kamar haka:

1- Hadin kai da tausayawa juna.

2- Kaucewa cutar da juna.

3- Taimakon juna akan gaskiya.

Addini da imani da Allah da ranar kiyama su ne zasu iya samar da wadannan ginshikai guda uku kamar yadda muka fada a sama.

Amfanin addini na farko a zamantakewa ko rayuwar al'mma shi ne samar da hadin kai sakamkon akida guda, sannan shi ne abu mafi tasiri wajen samar da so da  kauna a tsakanin mutane da kuma amince wa juna. Anan Allah T.A yana cewa:"ku riki igiyarAllah baki daya kada ku rarraba, sannan ku tuna ni'imomin da Allah ya yi a gareku yayin da kuka kasance makiyan juna ya hada zukatanku kuka wayi gari sakamakon ni'imarsa kuna "yan'uwan juna. Aali imran;103.

Daya daga cikin fai'dar addini  shi ne addini yakan kawar da  dukkan matsalolin dake damuwar al'umma wadan da sukan kai al'umma zuwa ga tabewa .

A kan haka ne Allah maigirma yake cewa: "Lallai Allah yana umurni da adalci da kyautatawa da kuma soyayya ga makusanta,sannan yana hani ga alfasha da abin ki da zalunci, yana yi muku wa'azi ne ko kun wa'aztu" Nahl:90

 Fa'idar addini ta uku ga al'umma, addini yana kira ga al'umma da kyautatawa da taimakon juna da alkhairi sannan da hadin guiwa wajen aiwatar da ayyukan da zasu amfani dukkan jama'a. sannan yana hanin alumma daga aikata dukkan abin da zai jawo wa al'umma masifa da shiga halin kaka na ka yi.A kan wannan ne Allah T.A yake cewa a cikin littafinsa mai tsarki." Ku yi taimakon juna akan bin Allah kada ku yi taimakon jun akan sabon Allah da zalunci, Sannan ku ji tsoron Allah, lallai Allah mai tsananin azaba ne.

 A tkaice addini yana kunshe da abubuwan da zasu kai ga al'umma baki daya zuwa ga cin nasara a rayuwarsu ta duniya da lahira.

Ya zuwa yanzu mun yi bayani kan bukatuwar mutane zuwa ga addini, don haka yanzu zamu koma zuwa ga asalin maganarmu wanda iata ce akidar shi'a a takaice. Amma kafin mu shiga cikin bayani kan akidojin dole a kula da wasu abubuwa kamar haka:

Dole ne mu samu yakini dangane da ginshikan addini:

Kamar yadda muka yi bayani a farkon littafan fiqh cewa dole ne kowane mutum ya samu yakini da tabbas a kan dukkan abin ya shafi akida ba kawai ya dogara ba da abin da wanin sa ya gaya masa ba. Wato dukkan abin da  ya shafi akida dole ne mutum ya yi bincike daya bayan daya ta hankali da nassin kur'ani da hadisi har ya samu yakini. Ba kamar fiqhu ba wanda mutum yana iya dogara da maganar wani malami masanin fiqhun , ba dole ne ba sai ya je ya gano aya ko hadisi wanda yake magan akan wannan abin,  fadar malamin  da yake taklidi da shi kawai ta isar masa hujja a wajen Ubangiji.Amma  dangane da akida ba haka ba ne, wajibi ne ga kowa ya tabbatar da gaskiyar ginshikan addini ta hanyar hankali ko nassi kamar yadda muka yi bayani  a sama.

Me ya sa  ba a taklidi a cikin akida?

Abin da yasa malaman addini musamman marja'ai suka ta fi akan cewa ba 'a yin taklidi a cikin akida, taklidi ya takaita ne kawai akan abin  da ya shafi hukunce-hukunce

Saboda kamar yadda ayoyi da ruwayoyi suka zo  akan cewa, lallai mutum wajibi ne ya samu yakini akan abin da ya shafi akida, ta hanyar taklidi kuwa ba za' a iya samun yakini ba, domin kuwa malami idan ya gaya maka cewa, misali dariya tana bata salla kuma ka yi aiki da shi anan ba wai yakini ka samu ba akan hakan duk da cewa idan ka yi aiki da hakan ya yi, amma ba ka samu tabbas ba, kawai ka dogara da shi ne domin ka san baya yin karya. Amma idan kana so ka samu yakini shi ne ka je ka yi bincike da kanka har ka gano inda Allah ya yi umurni da hakan, sannan ne ka samu yakini akan hakan.To a cikin abin da ya shafi hukunce-hukunce an yi mana rangwame cewa muna iya yin koyi da wasu masana akan hakan . Amma abin da  ya shafi akida dole ne mu yi bincike da kammu har mu gano hakan. Urwatul wuthka: babin taklidi mas'ala ta 65.

Suratul  Nahl:106--- Hujuraat:14 dukkansu suna dauke da bayanin hakan.

Ban da ma hakan samun yakini  akan abin da  ya shafi akida yana daya daga cikin siffofin kamala na ruhi mutum ta yadda zai san abin da shafi Allah da siffofinsa madaukaka. Sannan yakan fitar da ruhin mutum daga cikin duhun jahilci zuwa hasken ilimi wanda hankali yana umurtar mu da yin hakan kuma yakan lissafa shi cikin siffofi kyawawa.



back 1 2 3