Akidojin Shi'a



 Fa'idojin addini:

Fa'idar addini ta kasu zuwa gida biyu:1-Fa'idarsa ga mutum a matsayinsa shi kadai ba tare da la'akari da waninsa ba.2-fa'idarsa ga mutum a matsayinsa wanda yake rayuwa a cikin mutane.

Faidar addini ga  mutum a matsayinsa na shi kadai kusan a ce a bayyane yake, don haka muna iya takaitasu a cikin jumala guda uku.1-samar da natsuwa ga mutum.2-karfafa ruhin Dan-Adam.3-kare kutum daga sauran matsaloli.

Natsuwa: Amma dangane  da natsuwa ga mutum, Allah madaukaki yana cewa a cikin kur'ani,"Wadan da suka yi imani zuciyarsu tana natsuwa da ambaton Allah, lallai  ambaton Allah yana natsar da zuciya."ra'ad:28.

   Lallai daya daga cikin fa'idar addini ga ko wane mutum ita  ce, tana sanya mutum ya zama ya yi imani da Allah wanda yake shi ne, hakika wadda ba ta canzawa, sannan kuma shi ne mahaliccin kowa da komi wanda yake baiwa bayinsa ni'imomi marar karewa. Allah shi ne wanda dukkan alkhairai da rayuwa suke a hannunsa, yin Imani da haka ga mutum yakan sanya zuciyarsa ta samu natsuwa. Lallai duk wanda yake da Allah yana da komi, don haka wanda ya yi Imani da Allah ba ya tsoron komi sai shi kadai Allah madaukaki don shi kadai yake iya yin komi. Da haka ne sai mutum ya samu natsuwa ta musamman a cikin zuciyarsa.

 Karfin zuciya: Addini yakan sanya mutum ya zama yana da karfin zuciya ta yadda zai samu dammar ya fi karfin son zuciyarsa, Allah madaukaki dangane da iyalan Imam ali a.s. yana cewa: "Suna cika alkawalin da suka yi, sannan suna tsoron ranar da  sharrinta a warwatse yake. Sannan suna ciyar da abinci bisa suna son shi ga mabukata, marayu da bursunonin yaki. Lallai muna ciyar da ku saboda neman yardar Allah, kuma ba mu neman sakamako daga gareku  ko godiya." Dahr:7-9.

  Lallai  irin wadannan siffofin  suna samuwa ga zuciyar  mutum sakamakon addini ta yadda ruhin mutum zai yi karfi sannan ya samu imani da kudrar Ubangiji wadda ba ta gushewa, sannan ruhi mai rauni ba zaya taba iya samu irin wadannan siffofi ba na kamala. Ruhin da yake damfare da Allah shi ne  ruhi mai karfi wanda idan za'a dora rana a tafin hannunsa wata a bayan hannunsa ba zai bar abin da yake akai ba na madaukakin hadafi.

kariya ga mutum:daya daga fa'idojin addini shi ne, addini yakan  kiyaye mutum daga shiga wani hali na kaka na kayi wanda zai iya nisantar da shi daga siffofi na gari.Addini yakan kiyayen mutum wanda ya yi Imani da ranar kiyama daga dukkan abubuwan da Allah zai yi fushi da shi wanda sakamakon hakan zai zama mutumin banza a cikin al'umma.Saboda haka mumini  ba ya zaluntar kowa yana kiyaye hakkokin jama'a. Imam Ali a.s yana cewa:" Ina rantsuwa da Allah, in kasance ina kwana bisa kaya ko ina daure a cikin sarkoki ya fi mani soyuwa  akan in wayi gari ranar kiyama  in hadu da Allah da manzonsa ina matsayin na zalunci wani daga cikin bayin Allah ko na ci dukiyar wani ba tare da hakki ba. Imam ya cigaba da cewa da za'a bani sammai bakwai da abin ke cikinsu akan in kwaci fatar alkama dake bakin tururuwa ba zan amsa ba."

 Don haka addini yakan sa mutum ya maida al'amarinsa zuwa ga Allah wanda sakamakon haka ne zai samu natsuwa, da haka ne kuma zai samu kariya daga ayyukan assha.

 Lallai idan mutum ya kama addini gaskiya to lallai zai isa zuwa ga nasarar duniya da lahira wadda yake guri.Don haka addini yana da fa'idoji na duniya da lahira, wato mutum sakamakon addini zai samu nasarar rayuwarsa duniya da lahira.Addini yakan sa mutum ya zama yana dogara da kansa kuma ya samu karfin ruhi da natsuwa, sannan ya samu kariya daga munanan dabi'u. Sakamkon haka sai ya samu rayuwa mai kyau da kwanciyar hankali. Allah madaukaki yana cewa:"Duk wanda ya yi aikin kwarai namiji ne ko mace kuma alhalin yana mumini, to zamu rayar da shi rayuwa mai kyau, sannan kuma zamu saka masa da mafi kyau daga  abin da suka kasance suna  aikatawa."Nahl:98



back 1 2 3 next