Annabci



Ya sanar da mu yadda suka koma fito na fito da hakora ba da harshe ba, ya sanar da mu cewa shi Alkur'ani wani nau'i ne na mu'ujiza kuma Annabi Muhammad Dan Abdullah (S.A.W) ya zo da shi ne da kira da kuma da'awar sako don haka muka san cewa Manzon Allah (S.A.W.) ya zo da gaskiya da hakika kuma shi ma ya gaskata da su (S.A.W).

 Ismar Annabawa

Kuma mun yi imani da cewa Annabawa ma'asumai ne ba sa aikata sabo dukkaninsu, haka nan Imamai (A.S). Mun saba da wasu daga cikin musulmi a kan haka don su ba su wajabta isma (rashin aikata sabo) ga Annabawa ballantana ma Imamai.

 Isma: lta ce tsarkaka daga aikata zunubi da sabo kananansu da manyansu da kuma tsarkaka daga mantuwa koda kuwa hankali bai kore aukuwar haka daga Annabi ba, kuma wajibi ne ya tsarkaka hatta daga dukan abinda yake zubar da mutunci kamar cin abu a kwararo a tsakanin mutane ko kuma kyalkyala dariya da dai dukkan abinda bai dace a aikata shi ba a tsakanin mutane.

Dalilin da ya sa Isma ta zama wajibi kuwa shi ne idan da har ya halatta Annabi ya aikata sabo ko kuma ya yi kuskure, ko kuma wani abu makamancin wannan ya auku daga gare su to kuwa lalle da biyayya gare su a aikin da suka aikata da sabo ko kuskure bai wajaba ba, ko kuma da idan har ya wajaba to da mun halatta aikata sabo da dogaro da rangwame daga Allah, hasali ma dai mun wajabta haka kenan wannan kuwa abu ne tabbatacce a wajiban Addini da kuma a gurin hankali, idan kuwa biyayya gare shi ba ta wajaba ba a kan haka to kuwa wannan ya saba wa Annabci wanda babu makawa tana tare da wajabcin da'a da’imani. Idan kuwa ya zamanto duk abinda ya auku daga gare shi muna jin cewa imma daidai ne imma kuskure to bai wajaba a yi masa da'a a kan kome ba, sai fa'idar aiko Annabawa ta zamanto ta tafi haka nan kawai, Annabin kuma sai ya zama kamar sauran mutane, maganarsa ba ta da wata kimar da za a dogara a kanta da'iman kamar yadda biyayya gare shi ba za ta zama tilas ba. Ba ma za a sami kwanciyar hankali ba baki daya game da maganganunsa da ayyukansa. Wannan kuma dalili ne da ke tabbatar da cewa Isma na tare da Imami domin kaddara cewa shi zababbene daga Allah (S.W.T) don shiryar da mutane a matsayin halifan Annabi, za mu yi karin bayani a fasali game da Imama.

Siffofin Annabawa

Mun yi imani da cewa, Annabi kamar yadda ya wa.jaba ya zamanto ma`asumi haka nan ya wajaba ya zamanto yana da mafi kamalar siffofin dabi'u da hankali wadanda mafifita sune jarumtaka, da iya tafi da jama'a, da shugabanci da hakuri, da karfin kwakwalwa da hazikanci, har ya zamanto babu wani daga cikin mutane da zai yi kusa da shi a kan haka, domin ba don haka ba da babu yadda Annabcin ya zamanto shugabanci a kan dukan halittu kamar yadda ba zai yiwu ya zamanto ya tafi da al'amuran duniya baki daya ba.

kazalika wajibi ne ya zamanto mai tsarkin haihuwa dan halas, amintacce, mai gaskiya wanda yake tsarkakakke daga dukkan miyagun dabi’u hatta kafin aiko shi saboda zukata su amintu da shi rayuka kuma su juya zuwa gare shi hatta ma don ya cancanci wannan matsayi mai girma daga Ubangiji.

Annabawa da Littattafansu

Mun yi imani a dunkule da cewa dukan Annabawa da Manzanni a kan gaskiya suke, kamar yadda muka yi imani da kasancewarsu ma'asumai tsarkakakku. Musanta Annabcinsu kuwa, da zaginsu, da yin isgili da su yana daga kafirci da zindikanci, domin yin haka yana nufin karyata Annabinmu wanda ya ba da labari game da su da kuma game da gaskiyarsu.

Wadanda aka sani daga cikinsu kuwa kuma aka san shari'o'insu kamar Annabi Adam (A.S.) da Annabi Nuhu (A.S.) da Annabi Ibrahim (A.S.) da Annabi Dawud (A.S.) da Annabi Sulaiman (A.S.) da Annabi Musa (A.S.) da Annabi Isa (A.S.) da sauran Annabawan da Alkur'ani ya ambace su a sarari ya wajaba a yi imani da su a ayyane, duk kuwa wanda ya karyata daya daga cikinsu to ya karyata su baki daya kuma Ya karyata Annabinmu a kebance, haka nan ya wajaba a yi Imani da littafansu da abinda aka saukar musu

Attaura da Injila ko kuma Baibul Tsoho da sabon Alkawarin da ke hannnun mutane a wannan zamanin ya tabbata cewa gurbatattu ne daga zamanin wadanda aka saukar saboda abinda ya auku gare su na daga canje-canje da musanyawa, na daga kari da ragi bayan zamanin Annabi Musa da Annabi Isa (A.S.) saboda wasan da ma'abuta son rai da kwadayi suka yi da su. Bilhasali ma dai yawanci ko kuma ma dukkaninsu manya ne suka kaga su. bayan su Annabi Musa (A.S.) da Annabi Isa (A.S.) ba sa nan.

Musulunci

Mun yi imani cewa lalle Addini a gurin Allah kawai shi ne Musulunci kuma shi ne Shari'ar Ubangiji ta gaskiya wadda ita ce Shari' ar karshe kuma ita ce mafi kamala kuma mafi dacewa ga alherin bil Adama, ita ce ta fi kunsar maslaharsu ga al'amuran duniya da lahira, ita ce mafi dacewa duk tsawon zamani ba ta canjawa ba ta sakewa kuma matattara ce ga dukan abinda Dan Adam yake bukata daga tsarin rayuwar daidaiku da halin zaman jama'a da na siyasa.



back 1 2 3 4 5 6 7 next