Annabci



Abokin husumar rai da ke cikin zuciya da imani yana tsakanin aron raunanawa ne da kuma hankali duk wanda hankalinsa ya yi galaba a kan rauninsa to yana daga cikin mafi kololuwar matsayi masu shiryarwa a 'yan adamtakarsu, kammalallau a ruhinsu wanda kuwa rauninsa ya rinjaye shi to lalle yana daga cikin masu hasarar matsayi masu taraddudi a ‘yan Adamtaka masu faduwa zuwa matsayin dabbobi.

Mafi tsanani daga cikin wadannan masu husuma biyu ita ce tausasawar zuciya da rundunarta don haka ne kake ganin yawancin mutane sun dulmuye a cikin bata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin sha'awace-sha'awace da amsa kiran raunin zuciya,

"kuma mafi yawan mutane ba za su zama muminai ba koda kuwa ka yi kwadayin haka." Surar Yusuf: 103.

Shi mutum saboda gazawarsa da rashin saninsa game da abubuwan da ke kewaye da shi, da kuma rashin sanin asirran abubuwan da ke kewaye da shi da ma wadanda suke bullowa daga cikinsa shi kansa ba zai iya sanin dukan abinda zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa ba kuma zai iya sanin abinda zai kai shi ga samun sa'ada ko ya kai shi ga tsiyacewa ba Sawa’un a kan abinda ya kebantu da shi ne shi kadai ko kuwa wanda ya shafi dan Adam baki daya da kuma al'ummar da ke kewaye da shi.

Shi bai gushe yana jahili kuma yana kara jahilci ne ko kuma kara fahimtar jahilcinsa ne duk yayin da iliminsa game da dabi'a ko kuma ababan halitta ya kara karuwa, saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kaiwa ga darajar sa'ada yana bukatar wanda zai dora shi a kan hanya mikakkiya shararriya zuwa ga shiriya domin rundunar hankali ta kara karfafa da haka har ya zamanto mutum zai iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da raunin tausasawar zuciya.

Yawanci bukatar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara,na kara tsananta ne yayin da tausasawar zuciya ke yaudarar sa ta hanyar nuna masa abinda yake mummuna cewa mai kyau ne ko kum, kyakkyawa cewa mummuna ne ta nuna masa kyawun fandarewarsa,ta rikitar masa hanyar gyara da sa'ada da ni'ima a lokacin da shi ba shi ­da masaniyar da zai bambance dukan abinda yake mai kyau mai amfani da kuma wanda yake mummuna marar amfani.

Game da gaggawar kutsawa cikin wannan arangamar ne ta yadda ya sani kuma ta inda bai sani ba sai dai wadanda Allah ya kubutar,.Saboda haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani ya kai kansa ga dukan tafarkunan alheri da amfani da kuma sanin dukan abinda zai amfane shi ko ya cutar da shi a duniya da Lahira ballantana kuma jahili sawa'un al'amari ne da ya kebe shi shi kansa ko kuma ya hada da al'umma da yake zaune a cikinta ne, ba Ya taba kaiwa ga wannan masaniyar koda kuwa ya hada kai ya yi taimakekeniya da sauran mutane da ke tare da shi ko da kuwa sun hadu sun yi bincike, koda kuwa sun yi tarurruka da zama daban daban da kuma shawarwari.

Don haka ne ya zama wajibi Ubangiji ya aiko da Annabawa da Manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su.

"Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana koya musu littafi da hikima" (Surar Juma'a: 2)

 Yana musu gargadi game da abinda ke da cutarwa gare su kuma yana musu albishir game da abinda yake da alheri da gyaruwa da sa'ada a gare su. Tausasawar daga Allah  wajibi ne domin tausasawa ga bayinSa na daga cikin tsantsan kamalarSa. shi mai tausasawa ne ga bayinSa, mai yawan baiwa, mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da ya dace akwai bukatar ya kwarara kyautarSa da tausasawa to babu makawa ya zuba tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu nakasa da tawaya a kyautarSa da karimcinSa.



back 1 2 3 4 5 6 7 next