Yara a Cikin Shari'aImam Ali (a.s) yana fada a cikin wasiyyarsa ga dan sa Imam Hasan (a.s) cewa: “Hakika zuciyar yaro danye kamar kasa ce maras komai, duk abin da aka jefa mata sai ta karba, don haka sai na gaggauta tarbiyyarka kafin zuciyarka ta kekashe, hankalinka kuma ya shagaltu†[10]. Wata ruwaya ya zo cewa: “Ku ladabtar da ‘ya’yanku a kan abubuwa uku; son annabinku, da son ahlin gidansa, da karanta Kur'ani[11]. Wata ruwaya ta yi nuni da tarbiyyar yaka kamar haka: Koyar da littafin Allah, da koyar da harbi, da iyo a ruwa, da barin gadon dukiya ta halal[12]. Manzon rahama mai tsira da aminci yana cewa: “Duk wanda ya yi wa ‘ya aure, kuma ya aika ta gidan mijinta, to Allah zai sanya masa hular sarauta a kansa ranar kiyama[13]. Hafiz Muhammad Sa'id www.hikima.org hfazah@yahoo.com Sunday, November 15, 2009 |
back | 1 2 3 4 5 | next |