Cutarwa



Sai dai wannan kuma ba yana nufin nuna makauniyar so ga 'ya'ya ba, ta yadda wasu iyayen sukan kai 'ya'yansu su baro cikin halaka sakamakon nuna musu kauna maras kan gado. Imam Bakir (a.s) yana cewa: “Mafi sharrin iyaye shi ne wanda kyautatawa (soyayya) ta kai shi ga shisshigi (wuce gona da iri)”[8].

Amma wasu iyaye sukan yawaita tsine wa yaransu da mummunan zagi da kan iya kara wa yaro lalacewa, a tarbiyyar musulunci hatta dukiya, da tumaki, da kaya, da gida, da tufafi, da abin hawa, da matar mutum, an hana la’antar su don su zama masu amfani da alheri ga al’umma. Mu sani tsene wa yaro babu abin da zai kara masa sai kekashewa, da kangarewa, da lalacewa.

Maimakon su yi wa yaronsu addu’a da za ta gyara shi sai su yi ta yi masa mugun baki da mummunan fata, su sani duk wata tabewa da wahalar da hakan zai haifar ga yaro tasirinsa zai dawo ga iyaye a karshe, domin idan wannan tsinuwa ta bi shi ya lalace ba abin da zai same shi a duniya sai talauci da rashin albarka a kan duk abin da ya sa a gaba.

Bincika rayuwar irin wadannan yara da kullum iyaye kan tsine musu ka gani, zai wahala ka ga dayansu wanda ba ya fama da talauci ko tabarbarewa kan duk abin da ya sa gaba, saboda haka ya kamata iyaye su sani cewa lalacewar 'ya'yansu, su ne farkon wanda abin zai fara shafa.

Wani mutum da ya kai kukan ‘ya’yansa masu tsananin saba masa wajen manzon rahama (s.a.w), sai Annabi (s.a.w) ya tambaye shi cewa; Shin ka kyamace su ne (da mugun baki)? sai ya ce: Haka ne. sai Annabi (s.a.w) ya ce: Kai ne ka jawo tabewarsu. A wata ruwayar manzon rahama (s.a.w) yana cewa: “Ku kiyayi mummunar addu’ar iyaye, domin tafi takobi kaifi” [9].

Wasu jama'ar kuwa sun dauki zagi a matsayin al'ada, sai suka kasance hatta da fada ga yaro suna yin sa ta hanyar zagi ne. Irin wadannan mutane ya kamata su sani cewa; zagi koda sau daya faufau ba ya iya zama warwarar matsalar yaro ko hanyar tarbiyyarsa, yana zama sabanin yadda ake zato ne, domin zai kasance hanyar koya masa zagi ne.

Yana da kyau idan ka ga yaronka yana yin abin da kasan ba mai kyau ba ne ka nuna masa fushinka da rashin jin dadinka, ya san cewa wannan abin na iya bata maka rai da ba zai iya ganin murmushinka ba, amma a sani yana bambanta daga laifi babba da karami, sannan kuma da kula da bambancin da yake tsakanin yara gwargwadon shekarunsu, sannan kuma matakin farko ba shi ne ka fara dukan yaro ba domin ta yiwu shi a wajansa bai san wannan laifi ba ne, da ya sani watakila da bai aikata ba.

Idan laifin dan karami ne ko ba shi da tasiri wajan bata tarbiyya a nan ya isa ka yi masa nuni da shi cikin labaru, ko hani. Wato abin da yake bukatar tsanani a tsananta, wanda yake bukatar sauki a saukaka, ba komai tsanani, ko komai sassauci ba, domin wannan kuskure ne babba.

Haka ma wannan yana da bambanci tsakanin shekarun yara da suka bambanta, amma ma’aunai suna iya zama a gane su da hankali, kamar yaro dan shekara daya da rabi ya rika kiran sunan abokanka da sunansu domin ya ji kana kiran su da wannan sunan, a nan ba bukatar ka tsawata ka ce bai da ladabi domin bai ma san me kake nufi ba a nan, amma dan shekara bakwai yana iya gane wannan, akwai misalai masu yawa a kan haka.

Saboda haka a tsawata wa yara kada duka ya zama mataki na farko, wannan yana iya saba masa da dukan har ya zama ba ya magani, haka nan ma yana iya kasancewa shi a lokacin bai san wannan abin laifi ba ne. Sannan kada ka ga kai ka haife shi, idan ya zama akwai zaluntarsa, ko cutar da shi da daukar matakai sabanin na shari’a da hankali, Allah (s.w.t) zai yi maka hisabin rashin kiyaye amanar da ya ba ka.



back 1 2 3 4 next