CutarwaNa kasance daga cikin wadanda aka so su kasance masu bulala a wata furamare da na koyar amma sai na zabi in kasance mai bayar da tarihi da kissoshin salihan bayi ga yara, don haka sai na fi kowane malami farin jini. A bisa tajribar da na samu akwai lokacin da muka ki malamin lissafi saboda kyamar halayensa, kuma wannan ya sanya rauni a ilimin lissafin mafi yawancin dalibai. Wannan mummunar hanyar tarbiyya har yanzu tana nan a cikin makarantun addini musamman na karatun Kur’ani da aka fi saninsu da makarantun allo. Kamar yadda har yanzu akwai wata mummunar al’ada ta bakin zalunci a makarantun boko da aka fi sani da “Siniyoratiâ€, ta yadda daliban manyan azuzuwa sukan azabtar da na kananan azuzwa. Kamar yadda ya gabata cewa dukan yaro ba shi da kyau in ba wajan tilas ba, da kuma cewa zai yi amfani, haka ma daka wa yaro tsawa ba shi da kyau, domin yana iya haifar masa da ciwon tsoro ko ya firgita shi, abin da kan iya haifar masa da ciwo a jikinsa ko raunin zuciya. Kyamar yaro, da kushe shi, ko muzguna masa, da sukansa, da cin fuskarsa, suna daga cikin abubuwan da kan iya rusa himmar yaro, da azamarsa, da kuzarinsa, da tunaninsa, ta yadda za a sanya masa tunani da yakan kai shi ga rushe masa kwazonsa, da jin cewa; ba shi da hakkin bayyanar da ra’ayi. Takura yaro da bakanta masa rai, da dukansa ba ji ba gani, abubuwa ne da sukan sanya shi jin cewa yana bukatar ya girma domin ya zama mutum ya shiga sahun manya don ya huta da wannan nau’o'in azaba da gallazawa, ko ya sanya shi fadawa hanyar banza, ko daukar fansa da kece reni. A nan ne idan ya fusata kuma ya samu masu karbarsa kowane irin mutane ne, sai ya mayar da su abokansa ya kuma tasirantu da su. Irin wanann nau’i na tarbiyya ba komai a cikinta sai danne hakkin dan Adam, da rusa manyan gobe. Wasu mutane ko wasa suka ga yara suna yi sai su daka musu tsawa da zagi[4], kamar dai ba su taba jin fadin Allah a Surar Yusuf ba: “Ka bar shi tare da mu a gobe, ya ji dadi, kuma ya yi wasa, kuma lalle mu masu tsaro ne gareshiâ€[5]. Sau da yawa yara sukan ga irin wadannan mutane masu takura musu a matsayin mugwayen makiyansu. Su mutane ne masu bacin rai da bakin ciki da halayen yara kodayaushe, yara ba su isa su ga dariyarsu ba sai dai bakin cikinsu. Annabin rahama bai yardar wa muminai da wannan halin ba: Ya zo a wata ruwaya cewa; "Mumini shi ne wanda yake farin cikinsa yana fuskarsa, bakin cikinsa yana zuciyarsa[6]. An ce an yi wani mutum da ya hana yaronsa wasa ko kadan, sai yaron ya taso dolo, ba kuma abin da yake so sai wasa irin na yara, da ya kai shi wajan masana halin dan Adam sai suka gano ba a bar shi ya yi wasa yana yaro ba, saboda haka suka umarci uban da ya sayo masa kayan wasa. Haka nan ya yi ta wasa har wata rana da kansa ya bar kayan wasan, da iyaye suka ce ga kayan wasanka can sai ya ce: Ai ni ba karamin yaro ba ne, ta haka ne a ka yi maganin matsalarsa. Wasu ruwayoyi sun yi nuni da tausaya wa yara da nun jin kai garesu; Manzon rahama (s.a.w) mai tsira yana cewa: “Duk wanda ya sumbanci dansa to Allah zai rubuta masa kyakkyawa (lada)â€[7].
|