Boyayyar TaskaSarakunan lokacinsa: Al-mutawakkil da Al-mustansir da Al-musta’in da Al-mu’utaz da Al-muhtadi da Al-mu’utamad. Tarihin shahadarsa: 8 Rabi’ul Awwal 260 H. Inda ya yi shahada: Samra’u. Dalilin shahadarsa; An kashe shi da guba a lokacin Al-mu’utamad. Inda aka binne shi: a gidansa na Samra’u a Irak. Muhammad Dan Hasan Al-Mahadi (A.S) Sunansa da Nasabarsa: Muhammad dan Hasan dan Ali dan Muhammad (A.S). Babarsa: Kuyanga ce Mai suna Narjis. Kinayara: Abul Kasim. Lakabinsa: Al-Mahadi, Al-muntazar, Sahibuz Zamani, Al-hujja, Al-ka’im, Waliyyul Asri, Assahib. Tarihin haihwarsa: 15 Sha’aban 255 a lokacin Al-mu’utamad. Inda aka haife shi: Samra’u.
|