Auren Mace Fiye Da Daya



Duba ka gani kafin ka sami namiji da yake kin matarsa a kwanciya ka samu mata masu yawa da suke hakan, shi ya sa kur’ani mai girma a maganar Nushuzi[6] bai yi maganar namiji ba sai mace yana mai cewa: “…Wadannan da kuke jin tsoron kaucewarsu ga shimfidarku…”[7]. Amma mace saudayawa takan ki mijinta a shimfida, a kan haka ne shari’a ta ce: Idan ta ki shi sai ya yi mata nasiha, idan ba ta bari ba sai ya kaurace mata a shimfida, idan ta ki ladabtuwa sai ya dake ta dukan da ba mai cutarwa ba.

Wadannan dokoki shari’a ta gindaya su ne domin maganin fasadi da hana kai wa ga zinace-zinace, wannan ne ya sanya shari’a ta saukaka wa mutane kuma ta bayar da mafita ga sha’awarsu, ta shar’anta yin auren mace fiye da daya ko auren mutu’a[8].

Shi ya sa Allah ya sanya haddi ga zina don babu laifin da yake da haddi sai ka ga ya bayar da mafitar da zata hana aikata shi, In ba haka ba yaya Allah zai sanya haddi kan abin da mutum ba zai iya ba!?

Sa’annan mace duk wata tana haila, wata matar tana haila kwana goma ko bakwai a kowane wata, sannan idan ta samu ciki wata tara ba ta shawar namiji sai kadan, a wannan yanayi wata tana yarda da shi ne saboda kar ta saba umarnin Allah, kuma idan ta haihu tana shayarwa a tsawon shekaru biyu ba kasafai ta damu da namiji ba, sannan rashin lafiya da tayiwu a shekara kwana talatin ba ta da lafiya, ko ta yi tafiya, ko ziyarar iyaye, ko wasu yan’uwanta, hada da aikace-aikacen gida da kan iya wahalar da ita kullum.

Saboda haka a shekara hudu sai ka cire kwana goma na kowane wata wato wata hudu na haila ka ga saura shekara biyu da wata takwas, Sannan ka cire shekara biyu na shayarwa ga wata tara na ciki, ka ga ke nan har sai mun aro wasu kwanaki za a samu kwanakin da take neman mijinta yadda ya kamata da halinta. Koda yake ba dole ba ne kowace mace ta zama hakan ba amma muna magana kan dabi’arta ne, amma namiji shi kodayaushe a sake yake, kuma yana iya samun bayyanar dabi’ar sha’awa matukar ya huta ko hankalinsa ya kwanta.

Rashin Fahimtar Ma’anar Yin Azumi

Akwai wasu jama’a da suka yi kokarin kauce wa sha’awarsu da yakar ta, amma sai ga irin wadannan mutane sun zama manyan maciya amanar al’umma, su ba su bar mace kowace iri ce ba har matan aure, wannan kuwa jama’a ce da ta kirkiro Rahbaniyanci. Haka ma wasu suka kirkiro shi a musulunci amma kamar yadda fada-fadan coci suka kasa kiyayewa su ma haka nan suka kasa.

Duba ka gani mana a Amurka shekarar nan ta 2002-3 kaga irin abin kunya da ya faru a coci-coci har ma aka sallami wasu daga malaman coci saboda abin kunya. Haka nan ka duba kasashenmu ka bincika kasha labari da mamaki a kan rayuwa ta irin masu Sufanci da Rahabaniyanci na karya da kuma yakar dabi’ar da Allah ya halitta a tare da su da kasawar mafi yawancinsu.

Akwai mai ganin sai ya yi ta yin azumi ya hakura ya kaurace wa sha’awarsa. Sai aka ce da shi: Don Allah in ka kai azumi ka sha ruwa ka huta yaya kake ji? ya ce: Wallahi shi wani lokaci yana kara jin sha’awa ne ma. Aka ce: To me ya sa kuka ce: Ya yi azumi? Sai suka ce: Akwai hadisi. Sai aka ce: Wasu malamai sun tafi a kan cewa ba haka ne manufarsa ba, domin wanda aka danganta hadisin gareshi ya yi aure kuma ya yi azumi.

Azumin tasirinsa shi ne lokacin da kake cikin yunwa ba lokacin da ka sha ruwa kuma ka huta ba, ko ba komai ya yi karo da Ayar Kur’ani. Domin a watan azumi ne suke zuwa ga matansu da dare a lokacin Manzon rahama (S.A.W), sai aka saukar da aya cewa: “…Allah ya san cewa hakika kuna ha’intar kawukanku… a yanzu ku zo wa matanku…[9]”[10]. Sai aka halatta musu zo wa matansu da dare. Sannan mun gabatar da misalai game da masu Rahabaniyanci da Sufanci.

Wani Dalilin Sakamakon Bincikena

Namiji nagetib ne ita kuwa mace pozitib ce saboda haka nagetib yana iya karbar komai aka zuba masa, shi ya sa ma sakamako dole ya bi shi kamar yadda yake a ka’idar Mandik. Amma mace pozitib ce tana da iyaka saboda haka ne ma dole shi ne za a iya ba damar auren mace sama da daya domin shi nagetib ne, dalili kuwa shi ne:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next