Auren Mace Fiye Da DayaAbin da suke tsoro na biyu shi ne; Kada ‘ya’yan waccan su zama abokan gabarsu, abin da wajanmu aka sani da ‘yan uba, wannan al’amari da an yi tunani da al’amari ne na kaunar juna da karfafa soyayya da gina al’umma ta gari. Kuma a nan iyaye mata ne ya kamata su taka babbar rawa domin gyara kamar ta hanyar renon ‘ya’yan juna da wanka da sauransu, wannan kuma shi ne hanyar gina al’umma mai kyau mai hankali da ci gaba. Saboda haka wannan sukan ya nuna masu sukan ba su da tunani mai fadi game da duniyar musulunci kuma suna da tsukakkiyar kwakwalwa ne, in ba haka ba da sun duba da mai ganin, kuma wannnan yana nuna mana cewa mace a kan kanta bisa dabi’arta ba abin da yake hana ta zama da kishiya. Amsar Suka Na Biyu
Da kuka ce: Dabi’a ta daidaita namiji da mace a yawa da adadi sai na ce: Na daya kun cire Allah cikin maganarku kun sanya shi gefe domin mu a wajenmu Allah ke halitta kuma ya tsara yadda halitta zata kasance. Na biyu: Ku lissafa mata da maza na kasarku ku fadi gaskiya su wa suka fi yawa, Idan kun ga mata sun fi yawa to ku tabbata maganarku game da dabi’a ba daidai ba ne, kun ga kun karyata kanku kuma dabi’a ta karyata ku kenan. Akwai Bambanci Ta Wani Bangare
Sannan a wajanmu al’amarin aure bai tsaya Na daya: Balagar tunani da isa aure yafi sauri ga mace a Na biyu: Kidaya ya nuna mata sun fi maza dadewa da tsawon rai wanda ya sanya adadinsu Na uku: Dabi’ar haihuwa ga namiji tafi ta mata, yawancin mata suna daina haihuwa ne a shekara hamsin amma namiji yana iya kai shekara dari da wannan sifa ko tamanin wato kusan ninkin na mata, wannan kuwa yana nufin ba abin da zai hana namiji yin aure domin a samu ci gaba da haihuwa idan da bukatar haka da kuma yardar su matan. Na hudu: Bala’oin da suke rage al’ummar kasa sun fi shafar namiji kamar yaki da sauransu. Idan ka yi kokwanto tafi kasar da aka yi yaki ka ga abin mamaki kamar Farisa, ka gani mata nawa ne kuma maza nawa ne? Idan ka fito (koda yake ya hadu da al’adunsu) ka tsaya a titi ka kirga mata nawa kafin ka ga maza nawa. Ka ga mata sun kai shekara talatin zuwa arba’in kai wata har ta mutu babu miji, kuma ga wasu masu yawa da mazansu sun mutu ne amma saboda al’ada sun kasa samun yin wani auren. Ta haka ne matsaloli suka yawaita, ko dai su yarda da auren mace fiye da daya su jefar da al’ada, ko dai ya zama an ci gaba da zama haka nan wasu matan suna gani su mutu da bakin cikin rashin miji.
|