Imamanci Da Nassi2



Bayan ambaton hakkin jagoranci, wannan al’amari wani abu ne da imam Ali ya yi bayaninsa a fili ko ya yi nuni[50] da shi, amma sai ga shi irin su Dakta Ammara yana neman ya gafala daga wannan hudubobi na imam Ali (A.S) yana neman nuna rashin samun magana ta karara a kan hakan, Da kuma neman kare kagen da ya yi domin ya nuna kalmar “wasiyyiâ€‌ da ta zo a hadisud dar, da cewa kage ne na Shi’a da suka sanya kalmar wasiyyi maimakon waziri[51] alhalin hadisin da ya zo daga ruwayar Ahlussunna bai zo da wata kalma ba in banda kalmar wasiyyina[52].

3- Hadisin “shugabanni daga kuraishawa ne, kuma suna cikin Bani Hashim, ba na waninsu ba ne, kuma shugabanci ba ya yiwuwa ga waninsuâ€‌[53]. Mun riga a baya mun yi nuni da wasu hadisai da suka nuna duk wani fifiko da cancantar Bani Hashim a kan sauran kuraishawa.

4- Fadinsa (A.S): “Ina zaku ne! Yaya kuke kirkirar karya! ga hujjoji a fili, ga ayoyi karara, ga manarori a kafe, yaya ake dimautar da ku?! Yaya kuka makance alhali a cikinku akwai zuriyar annabinku, su ne jagororin gaskiya, kuma alamomin addini, harsunan gaskiya?! Ku sanya su a matsayi mafi kyau na Kur’ani, ku kuma gangaro zuwa garesu irin gangarowar nan ta mai kishirwa. Ya ku mutane ku rike ta daga cikon annabawa (S.A.W) cewa: Duk wanda ya mutu daga cikinmu ba matacce ba ne, kuma duk wanda ya rididdige a cikinmu ba rididdigagge ba neâ€‌[54]. A cikin wannan akwai abin takaici da imam (A.S) ya yi nuni da shi ga wadanda suka bar Alayen Annabi (A.S) bayan hujja da dalilai masu karfi, bayyanannu da suke wajabta bin su.

5- Fadinsa: “Mu kama ce ta tsatson ma’abota jirgin ruwa, kamar yadda wanda yake cikin can ya tsira haka ma wanda yake cikin wannan zai tsira, azaba ta tabbta ga wanda ya bar mu… kuma ni a cikinku kamar kogo ne na As’habul kahafi, kuma ni kamar kofar hidda ce, da wanda ya shige ta ya tsira wanda ya ki shiga ya halaka, ni hujja ce daga watan zilhijja a hajjin bankwana da fadin Annabi (S.A.W) cewa: “Ni na bar muku abin da idan kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba a bayana har abada; littafin Allah da kuma Ahlin gidanaâ€‌[55].

6- Hudubarsa (A.S): “Ku duba Ahlin gidan Annabinku, ku lizimti tafarkinsu, ku bi sunnarsu, ba zasu taba fitar da ku daga shiriya ba ba kuma zasu taba dawo da ku cikin bata ba… idan suka yi kasa ku yi kasa idan suka tashi ku tashi… kada ku riga su sai ku bata, kada ku yi jinkirin binsu sai ku halakaâ€‌[56].

7- Fadinsa (A.S): “… shin ban yi aiki a cikinku da alkawari mafi girma ba, kuma na bar muku (na yi muku wasiyya da) alkawari mafi karantaâ€‌[57]. Alkawari mafi girma shi ne Kur’ani, alkawari mafi karanta su ne Ahlul Baiti (A.S) da su ne imam Ali (A.S) da Fadima (A.S) da imam Hasan (A.S) da imam Husain (A.S).

8- Fadinsa (S.A.W): “Mahadi daga cikinmu yake Ahlul Baiti, Allah zai tayar da shi a dare dayaâ€‌, Ahmad da Suyudi sun rawaito shi daga Ali (A.S)[58]. Da fadinsa: “Mahadi daga garemu yake â€کya’yan Fadimaâ€‌, Suyudi ya karbo shi daga Ali (A.S)[59]. Haka nan wadannan ruwayoyi suka zo game da Mahadi daga hadisai masu yawa, da bayanai a fili, da ishara da siffa, da kuma bayanin tarihi tabbatacce.

A takaice muna iya cewa matakin imam Ali (A.S) da yakininsa na hakkinsa a game da halifanci ya kasance yakini ne wanda yake ya samu daga matsayinsa gun Annabi (S.A.W) da kuma rayuwarsa ta hidima ga musulunci, hakika ya kasance a rayuwar Manzo (S.A.W) yana cewa: Allah madaukaki yana cewa; “Idan ya mutu ko aka kashe shi sai kuka juya a kan dugaduganku[60] (kuka bar tafarkinsa)â€‌, Imam Ali (A.S) yana cewa: “Wallahi ba zamu juya a kan dugaduganmu ba, bayan Allah ya shiryar da mu, wallahi idan ya mutu ko aka kashe shi, sai na yi yaki a kan abin da ya yi yaki a kai har in mutu, wallahi ni ne dan’uwansa kuma waliyyinsa dan amminsa mai gadon iliminsa, wanene ya fi cancanta da shi fiye da niâ€‌[61].

A wani wajen Ali (A.S) yana cewa: “Yayin da ya rasu sai musulmi suka yi jayayya a kan mulkinsa bayansa, wallahi bai taba fado mini ba, ban kuma taba tunanin cewa larabawa zasu kawar da wannan jagoranci a bayansa daga Ahlin gidansa ba! ban taba tsammanin za a kawar da shi daga gareni ba bayansa! sai ga mutane sun yi dafifi ga wane suna yi masa bai’a…â€‌[62]. Ashe kenan yana nufin hakkin da mutane suke nemansa, shi kuma ba ya rigonsu zuwa ga nemansaâ€‌[63].

Game Da Bai’ar Imam Ali (A.S) Ga Halifofi Uku

Sun kawo matsalar cewa imam Ali (A.S) ya yi wa halifofi uku bai’a, suka raya cewa wannan bai’ar kuma ba zai yiwu a ce domin maslaha ya yi ta ba, ko domin takiyya, ko tilastawa, domin wannan yana nuna tauye matsayi na imam Ali (A.S).  Amsar da zamu bayar ita ce: Game da tilasta shi wannan abu ne a fili, da masu tarihi suka rawaito.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 next