Imamanci Da Nassi2Suka ce: A’a. Ya ce: A cikinku akwai wanda Manzo ya ce: Duk wanda nake shugabansa wannan shugabansa ne in ba ni ba? Suka ce: A’a. Ya ce: Acikinku akwai wanda Manzo (S.A.W) ya ce: Kai a wajena kamar matsayin Haruna ne gun Musa, in ba ni ba? Suka ce: A’a. Ya ce: Shin a cikinku akwai wanda aka amincewa ya isar da surar bara’a kuma Manzo ya ce: Kuma ba wanda zai isar daga gare ni sai ni ko wani mutum daga gareni, in ba ni ba? Suka ce: A’a. Ya ce: Shin ba ku sani ba cewa sahabban Manzo sun gudu sun bar shi a filin daga[39] ba wanda ya rage tare da shi in ba ni ba, ban taba guduwa ba? Suka ce: E. Ya ce: Shin kun sani cewa ni ne farkon musulunta?
|