MA'ANAR AL'UMMA



Ba ma kawai wannan ba, Uwa na taimakawa wajen bunkasa al'umma da gina ta a tunani, abin duniya, da dabi'u ta hanyar tarbiyyantarwa da fuskantar da su; domin yaron da ya tashi nesa daga kunci da damuwar rai da matsalolin iyali, zai tashi mai mikakkiyar mutuntaka, mai kyakkaywar alaka da mu'amala da wasu, haka mai bayar da gudummawa mai kyau ga al'umma. Sabanin yaron da ya tashi cikin yanayin iyali da ke cike da matsaloli da tashe-tashen hankula da mummunar mu'amala ga yaro, irin wannan zai tashi ne birkitaccen mutum, mai adawa cikin dabi'u da alakokinsa; don haka ne ma mafi yawan halayen laifuka da mujirimanci cikin al'ummu na samo asali ne daga mummunar tarbiyya.

Akwai kuma wani fage daga fagagen ginin al'umma da Uwa ke taka rawa a cikin shi kamar yadda uba ke takawa, wannan kuwa shi ne fagen tarbiyya mai kyau. Yaron da ke tashi a bisa son aiki da kiyaye lokaci, ake fuskantar da shi fuskantarwa ta karantarwa mikakkiya ta hanyar iyali, kuma yake ci gaba da karatunshi, kuma yana gina iyawarsa na kirkire-kirkire, zai zama wani da ake amfana da shi ta hanyar abubuwan da yake samarwa na kwarewa da sannai na ilimi. Sabanin malalacin yaron da iyayenshi ba sa kwadayin fuskantar da shi ga aiki da samar da wani abu, domin shi zai zama na'ura ga wasu, kuma irin wadannan na haifar da ci baya mai yawa da ta6ar6arewar samar da abubuwa da daskarewar rayuwar zamantakewa, tattalin arziki da ilimi.

Haka fagagen gini ke kulluwa tsakanin tarbiyya, samarwa da bunkasar tattalin arziki, halayya da zaman lafiyar al'umma, kuma irin gudummawar mace wajen ginin zamantakewa na bayyana a dukkan wadannan fagage.

TUBALAN GININ AL'UMMA

Alaka tsakanin daidaikun mutane a rayuwar zamantakewa kamar alaka ce tsakanin haruffan (wani) harshe, matukar wadannan haruffa ba su hadu ba kuma an tsara alakokin da ke tsakaninsu ba, gamammen ginin harshen ba zai samu ta yadda zai dauki tunanin mutum ya suranta jiyayyar rayuwar mutum gaba dayanta ba.

Haka ma daidaikun mutane, ba sa daukar siga ta mutuntaka da hada al'umma da ke da samuwarta da tushenta da ya bambanceta daga samuwa da tushen daidaiku sai sun shaje da wasu alakoki, sun tsaru da alakokin da ke tsara harkokinsu da halayensu, wadannan alakoki su muka sammata da Tubalan ginin al'umma, wadannan kuwa su ne:­

1-Akida: Alakar akida na daga mafi girman alakokin dan Adam wadanda ke hada daidaikun mutane ta mayar da su abu daya da ke hade kamar jiki daya; kamar yadda hadisin Annabi ya nuna haka da nassinshi:­

"Za ka ga Muminai cikin tausayin junansu da kaunar junansu da jin kan junansu kamar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta koka, sai sauran sassan jiki ya dauki zazzabi da hana barci".3

Akida na da tasirorinta da abubuwan da take haifarwa na halayya da jiyayya a aikace cikin alakokin mutane baki dayansu, kuma tasirorinta na fadada daga gini zuwa kyautatuwa da kiyaye ginin zamantakewa; don haka za mu sami AIkur'ani mai girma yana bayyana wannan alaka da cewa:­

"Muminai maza da Muminai mata kuwa masoya juna ne; suna horo da aikata alheri suna kuma hani da mummunan alkl.." Surar Taubati, 9:71.

Wannan aya mai albarka tana tabbatar da akidar kauna tsakanin maza da matan da suka yi imani da Allah Madaukaki da sakonSa, haka nan tana tabbatar da ka'idar tunani da halayya da suka fi kowace ka'idar ginin zamantakewa karfi. Mace na shiga cikin wannan alaka a matsayin wani tubali na asasi, kamar yadda ya zo cikin nassin AIkur'ani, tana shiga cikin da'irar soyayya, kuma tana daukar alhakin gini, sauyi da kawo gyara ga zamantakewa kamar yadda namiji ke daukar na shi daidai wa daida; wannan na bayyana karara cikin nassin AIkur'ani da ambaton shi ya gabata a baya.



back 1 2 3 4 5 6 7 next