MA'ANAR AL'UMMA"..kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima..." Surar Zukhrufi, 43:32. A bisa wannan asasi ne ayyukan zamantakewa ke faruwa, kuma (haka) ya fassara tubalin faruwar ayyuka a cikin al'umma don rayuwa ta sami cika kamar yadda gabubban jiki ke cika wajen cika ayyukansu. Haka nan AlKur'ani ke yi mana bayanin abubuwan da ke haifar da al'umma, mutuntaka da abin duniya. Kuma cikin dukkan wadannan tubaloli da asasai, gudummawar mace na bayyana karara tun daga tushe, sawa'un ta bangaren abin duniya ne ko ta halayya ko aiki cikin rayuwar zamantakewa, ita babbar sashi ce ta al'umma. Hakika alkaluman mutanen duniya baki daya na nuna cewa adadin mata a duniyar dan Adam ya wuce adadin maza. Ta wannan hange na cikan aiki da AIkur'ani ya bayyana a baya, za a iya ginin gudummawar mace kamar yadda ake ginin gudummawar namiji daidai-wa-daida cikin tsaikon manufofi da halayyar Musulunci, mace ba asasi ta biyu ba ce, ba kuma karin halitta ba ce, duk kuwa da cewa jarabce-jarabcen dan Adam sun tabbatar da cewa gudummawar namiji wajen gina ilimi da tattalin arziki ya fi gudummawar mace zurfi da yawa kuwa, amma nata gudummawar wajen hada shika-shikan ruhi don gina iyali ya fi gudummawar namiji girma nesa ba kusa ba kuwa. wannan shi ne abin da AIkur'ani ya nuna da cewarsa: "..Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami natsuwa da ita". Surar A'arafi, 7:189. Ke nan namiji shi ne yake natsuwa zuwa ga mata, ya sami tabbaci da rayuwa tare da ita, ita ce cibiyar haduwa kuma tsaikon aminci, kauna da soyayya. AIkur'ani na magana a kan 'natsuwa' a wurare da yawa, ta nan za mu iya fahimtar ma'ana irin wadda mace kan samar ga mijinta, za mu fahimce shi ta hanyar fadarSa Madaukaki: "Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku.." Surar Rumu 33:21. Da fadarSa: "..Ya kuma halicci matarsa daga jikinsa don ya sami natsuwa da ita". Surar A'arafi, 7:189. Za mu fahimci kimar kalmar `Natsuwa' a zaman tare ne yayin da muka san cewa AIKur'ani ya siffanta alaka tsakanin miji da mata da cewa alaka ce ta (Natsuwa, kauna da soyayya). Ke nan bari mu karanto kalmar `natsuwa' a wurare da dama cikin AIkur'ani, don mu san ma'anarta a zamantakewa da iyali. Allah Madaukaki ya fadi cewa:"(Allah) Ya sanya muku dare a natse"
|