MA'ANAR AL'UMMAMA'ANAR AL'UMMA
AI'umma: na nufin tawagar nan ta mutane da ta hadu daga daidaiku, wadanda alakokina akida da amfanonin rayuwa iyakantattu suka hada su. Idan har wannan ne gamammiyar ma'anar al'umma, to al'ummar Musulmi ita ce wannan al'umma wadda ake gina alakokin kuma ake tsara amfanoni a cikinta bisa asasin Musulunci. Za mu iya ta'arifin al'ummar Musulmi da cewa: "Taron Jama'ar da a siyasance suke zaune a wani lungu na kasa, wadanda suka yi imani da Musulunci, kuma ake tsayar da alakokinsu da tsarin rayuwarsu a bisa asasin Musulunci".1 Don haka al'ummar Musulmi al'umma ce ta akida, wadda ke da abubuwan da suka kebanta da ita da siffofinta da ke bambanta ta da wasunta na daga al'ummu. Ita al'umma ce da ta kebanta da tunane-tunanenta, halayenta, dokokinta, tsarin rayuwarta, dabi'unta da sannanta. Hakika AIkur'ani mai girma ya takaita wadannan siffofi da cewa: "Rinin Allah, ba kuwa wanda ya fi Allah iya rini, kuma mu Shi muke bautawa". Surar Bakara, 2:138. Mafarin AI'umma Daga cikin al'amura na asasi da babu makawa a kan karanta su, binciken su da bin diddiginsu a ilmance, akwai mas'alar nan ta tashin al'umma da rayuwar zamantakewa, da sanin dalilai da musababbin shi (tashin); saboda abin da ke cikin na murdewa da haduwa da alakoki. Don bayyana ra'ayin Musulunci game da tashin al'umma da haduwar rayuwar zamantakewa, bari mu karanta abin da ya zo daga ayoyin AIkur'ani wadanda ke magana game da sha'anin zamantakewa, kuma suke kira zuwa ga ginin al'ummar dan Adam, da rina rayuwar mutum ta hanyar hada gamammen zaman tare bisa asasai karfafa da akidu tabbatattu; ga wasu daga cikin ayoyin kamar haka: "Ya ku mutane, hakika Mu Muka halicce ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku al'ummu da kabilu (daban-daban) don ku san juna, hakika mafi girmanku a wurin Allah shi ne wanda ya fi ku tsoron Allah..." Surar Hujarati, 49:13. "Akwai daga ayoyinSa Ya halittar muku mata daga kanku, don ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya kauna da tausayi a tsakaninku, lalle cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke tunani." Surar Rumu 33:21. "Shin su ne za su raba rahamar Ubangijinka? Mu ne muke raba musu arzikinsu a rayuwar duniya, kuma muka daukaka darajojin sashinsu a kan wani sashi don wani sashin ya riki wani mai yi mishi hidima; rahamar Ubangijinka kuwa, ita ta fi abin da suke tarawa (na duniya)." Surar Zukhrufi, 43:32.
|