Kaunar Juna4. Mas’alolin Ali dan Ja’afar: daga Ali dan Ja’afar ya ce: Na ce da Abul Hasan (A.S): Wane ne ya fi mu son addininsa? Sai ya ce: “Mafi tsananinku son sahibinsa†[8]. 1 / 2 Kimar Soyayya
A-Alamar Karfin (Kaifin) Hankali
5- Daga Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: Asasin hankali bayan imani da Allah madaukaki shi ne neman soyuwa wajen mutane[9]. 6- Daga gareshi (S.A.W): Neman soyuwa a wajen mutane ita ce rabin hankali[10]. B- Rabin Addini
7- Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Soyayya rabin addini ce[11]. C- Kusanci Mai Amfanuwa
8- Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Soyayya ita ce dayan makusanta biyu[12]. D-Mafi Kusancin Kusanci
9- Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Mafi kusancin kusanci shi ne soyayyar zukata[13]. 10- Daga gareshi: Da yawa makusanci ya fi nisa fiye da manisanci, kuma da yawa manisanci ya fi kusanci fiye da makusanci[14]. E-Asalin Kusancin (‘Yan’uwantakar Jini)
11- Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Da yawa (zaka samu) wani dan’uwa da ba mahaifiyarka ce ta haife shi ba[15]. 12- Daga gareshi: Abokinka shi ne dan’uwanka na uwa daya uba daya, ba duk wani dan’uwanka na uwa daya uba daya ba ne yake zama abokinka ba[16].
|