Soyayyar Juna“Wasu mata a cikin gari suka ce; matar sarki tana neman yaronta, kuma hakika soyayya ta mamaye ta, kuma mu muna ganin ta cikin so mabayyani. Yayin da ta ji makircinsu sai ta aika musu kuma ta tanadar wa kowacce daga cikinsu madogari kuma ta ba wa kowacce daya daga cikinsu wuka, kuma ta ce masa: ka fita zuwa garesu, yayin da suka gan shi sai suka girmama shi kuma suka yanke hannayensu kuma suka ce; girma ya tabbata ga Allah wannan ba mutum ba ne, wannan dai wani mala’ika ne mai girma†[5]. Hadisai: 243. Daga Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ce: -a fadinsa madaukaki- “Kuma hakika soyayya ta mamaye ta†hakika sonsa ya mamaye ta daga mutane, ba ta ganin waninsa[6]. 244. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: kada ku yi shawara da ma’abota soyayya; ku sani ba su da wani ra’ayi, kuma hakika zukatansu suna kunkuna, kuma tunaninsu yana bin juna, kuma hankulansu ziro ne[7]. 245. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya yi shaukin abu sai ya makantar da ganinsa, kuma ya sanya zuciyarsa maras lafiya, kuma yana kallo da idanuwa maras kyawu, kuma ya na ji da kunne maras ji, sha’awa ta keta hankalinsa, kuma duniya ta kashe zuciyarsa, kuma ransa ta damfaru da ita, shi bawa ne gareta, da kuma ga wanda wani abu nata yake hannunsa, duk inda ta gusa sai ya gusa tare da ita, kuma duk inda ta fuskanta sai ya fuskanta tare da ita, kuma ba ya tsoratuwa da Allah don wani ya tsawatar masa, kuma ba ya wa’aztuwa gabarinta daga wani mai wa’azi, kuma shi yana ganin masu riko da ita a kan rabauta[8]. 10 / 3 Mai Soyayya, Mai Kamewa
246. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: duk wanda ya yi kauna kuma ya boye, ya kame, ya yi hakuri, to Allah (S.W.T) zai gafarta masa kuma ya shigar da shi aljanna[9]. 247. Littafin Kanzul Ummal, daga ibn Abbas, Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: mafifitan al’ummata su ne wadanda suke kamewa idan wani bala’i ya zo musu na wani abu. Sai suka ce: wane bala’in? sai ya ce: soyayya[10]. 10 / 4 Mai So, Abin Yabo
248. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: mafificin mutane shi ne; wanda ya kaunaci ibada, sai ya rungume ta, ya so ta da zuciyarsa, kuma ya yi ta da jikinsa, kuma ya shirya mata, kuma ba ya damuwa a
|