Ladubban Zamantakewa



An tambayi Imam Ridha (a.s) dangane da ma’anar karimci (kyauta) sai ya ce: “Hakan cikin turaren da aka ba shi, da fadadawa a wajen zama, wanda ya ki su ya kasance kamar yadda aka ce[22]”.

A wasu ruwayoyin an kara matashi ciki da duk sauran abubuwan da ake girmama mutum da shi[23].

Tafarki Na Hudu: Girmamawa

Babu shakka dukkan yanayi na kyautatawa da alheri suna daga cikin ababen da suke nuni da kyakkyawar dabi’a da soyayya ga mutane, kamar yadda muka ga haka cikin ka’ida ta biyar, a nan gaba za mu yi karin bayani kan hakan yayin da za mu yi dubi cikin ka’ida ta biyar din.

Girmamawa da daukaka za su iya shiga cikin babin kyautatawa da alheri, to sai dai saboda alakan da suke da shi da batun haduwa da tarurruka, don haka yana da kyau mu ambato shi a wannan babin na (so da kauna) saboda sun kebanta da wannan babi ne.

Shari’a ta ba da kulawa ta musamman ta hanyar wasu hukumce-hukumce da ladubba, da mu yi nuni da wasu daga cikinsu:

Girmamawa

a) – Girmama abokai da daukaka su, an ruwaito Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Abu Ja’afar (a.s) ya kasance yana cewa: Ka girmama abokanka da daukaka su, ka da dayanku ya fada wa dayanku”.

A baya yayin da muke magana kan mu’amaloli na musamman mun yi ishara da batun girmama na gaba da masu yawan shekaru, da kuma cewa girmama su girmama Allah ne.

KarramaMusulmi Musamman Madaukakin Cikinsu

b) – Girmama madaukakan cikin al’umma, kai duk wadanda suka halarci wajen taro, mun ga wani sashi na hakan cikin babin karhancin mayar da kyauta. Haka nan girmamawar da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi wa Adi bn Hatam yana tabbatar da hakan. Amirul Muminina (a.s) yana cewa: “Lokacin da Adi bn Hatam ya zo wajen Annabi (a.s), Annabi ya shigar da shi gidansa, a lokacin babu komai a gidan in banda…..sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya mika su ga Adi bn Hatam[24]”.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Duk wanda ya karrama dan’uwansa mumini da wata magana da zai dadada masa da yaye masa bakin cikin da ke da shi, ba zai gushe cikin inuwar Allah ta rahana da aka shimfida masa ba matukar yana kan hakan[25]”.

Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Idan wani shugaban al’umma ya zo muku to ku girmama shi[26]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next