Ladubban Zamantakewa



Haka nan ba a so mutane biyu su kebance ko kuma yin kus-kus cikin magana alhali akwai wani na uku a tattare da su.

Haka nan rashin kyautatuwar katse mutum yayin da yake cikin magana, saboda “wanda ya nuna rashin amince da maganar musulmi yayin da yake cikin magana kamar ya ci fuskarsa ne[16]”.

LadubbanDariya

Na Hudu: Wasa (barkwanci) da dariya, a baya mun yi magana kan wajibcin kiyaye dariya da rashin kyaun kyalkyalcewa da dariya saboda abu ne abin ki; kamar yadda wani hadisi abin dogaro ya siffanta hakan da cewa lamari ne na Shaidan, da kuma bukatar takaita yawaita wasa da abubuwan ba da dariya, saboda hakan na zubar da mutumci da jan mutum zuwa ga kiyayya da gadar da gaba.

Duk da cewa sanya dariya da ita kanta dariyar abu ne mai kyau matukar ba a yawaita da kuma hada su da alfasha ba, saboda hakan na nuni da nau'i na so da kauna ne, da kuma dacewa da yanayi na ruhi da ran mai magana da wajen da ake zaune karkashin iyakokin ladubba na zamantakewa.

An ruwaito daga Mu’ammar bn Khallad ta hanya abin dogaro yana cewa: “Na tambayi Abal Hasan (a.s) na ce masa: Ya shugabana, mutum ne ya samu kansa cikin wasu mutanen da suke wasa da dariya, sai ya ce: babu laifi ga hakan matukar dai, sai na zaci yana nufin alfasha ne, daga nan sai ya ce: wani balaraben kauye ya kasance ya kan zo wajen Manzon Allah (s.a.w.a) ya ba shi kyauta, sannan sai ya ce masa: dakata ka ba mu kudin kyautarmu, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi dariya, kuma ya kasance idan yana cikin bakin ciki, ya kan ce: me balaranen kauyen nan yake? Ina ma da ya zo mana[17]”.

Kamar yadda kuma aka ruwaito daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Lalle Allah Na son wasa da dariya cikin jama’a amma ba tare da fasikanci ba[18]”.

Daga Yunus al-Shaibani ya ce: “Abu Abdullah (a.s) ya ce: Ya ya kuke wasa da dariya tsakaninku? Sai na ce: ba da yawa ba, sai ya ce: Ka da ku yi haka, saboda wasa da dariya na daga cikin kyawawan dabi’u, saboda kana shigar da farin ciki ne ga zuciyar dan’uwanka, Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance yana ba da dariya wa mutumin da yake son faranta masa rai[19]”.

Daga Fadhl bn Abi Kurra daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Babu wani mumini face sai yana da wasa da dariya (sanya dariya)[20]”.

KarbarKyauta

Na Biyar: yarda da karbar kyauta yayin da aka gabatar da ita ga mutum, saboda karbar na daga cikin nau’in so da kauna da kuma kyawawan dabi’u. Akwai hadisai masu yawa da suke kwadaitar da musulmi karbar kyauta da kuma cewa babu mai mayar da kyauta in ba jaki ba; kamar fadadawa ne a wajen zama da kaddamar da abin jingina (matashi) ga mutum, haka nan turare, da dai sauran duk wani abin da ake ba wa mutum saboda girmama shi a wajen taro ko kuma saduwa.

Abdullahi bn Ja’afar ya ruwaito cikin Kurbul Asnad daga Imam Sadik (a.s) daga babansa daga Ali (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Idan aka ba wa daya daga cikinku kyauta, to kada ya ki karba, saboda jaki ne ke mayar da kyauta[21]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next