Ladubban Zamantakewa



Tafarki Na Uku: Ladubban Zama da Tattaunawa

Tafarkin mu’amala yayin zama da tattaunawa da mutane na a matsayin tafarki na uku cikin batun kyawawan dabi’u da kyautatawa. A nan za mu ga shari’ar Musulunci ta bai wa wannan batu muhimmanci na musamman, da za mu iya ganinsu cikin wadannan abubuwa masu zuwa:

LadubbanZama

Na farko: Ladubban zama da tafarkin mu’amala a wajen zama da tarurruka na jama’a. Wadannan ladubba dai suna da yawa:

YalwatawaA Wajen Zama

a) – Yalwatawa da fadadawa a wajen zama (taro), haka nan yadawa, tashi da mikewa daga wajen zaman yayin kare taron, kamar yadda Alkur’ani mai girma ya ambaci hakan: “Ya ku wadanda suka yi imani! Idan an ce muku, ku yalwata, a cikin majalisai, to, ku yalwata, sai Allah Ya yalwata muku, kuma idan an ce muku, Ku tashi, to, ku tashi. Allah na daukaka wadanda suka yi imani daga cikinku da wadanda aka bai wa ilmi, wasu darajoji masu yawa…[1]”.

An ruwaito daga Imam Sadik (a.s) ya ce Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Yana da kyau a samu fili kimanin tsawon kashin damtse tsakanin mutanen da suke zaune a wajen zama don kada su takura da junansu[2]”.

Kamar yadda aka ruwaito daga gare shi (a.s) yayin tafsirin ayar ﴾إِنَّا نَرَاكَ مِنَ الْمُحْسِنِينَ ﴿ yana cewa: “Ya kasance ya kan fadada wajen zama, da ba da bashi ga mabukaci da kuma taimakon mai rauni[3]”.

Baya ga haka, za mu iya ganin jaddadawa kan wasu ladubban da Allah Madaukakin Sarki da Ahlulbaiti (a.s) suka yi, mai son karin bayani yana iya komawa ga littafin Wasa’il al-Shi’a.

Tarbada Ban Kwana

b) – Tarba da ban kwana ga mutumin da ya zo wajen taro, an ruwaito Abi Abdillah (a.s) ta sananniyar hanya yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: Daga cikin hakkin wanda ya shigo gida a kan masu gidan shi ne su taka masa suna masu maraba da shi idan ya shigo da kuma idan zai tafi[4]”.

MaiGida Shi Ne Shugaba

c) – Zama a inda mai gida ya ba wa mutum don ya zauna, saboda mai gida shi ya fi sanin wajen da ya fi dacewa a zauna a wajen, shin dangane da girmama bakon ne ko kuma dangane da sha’anin da ya shafi mai gidan. An ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Idan wani daga cikinku ya shiga wajen dan’uwansa musulmi a gidansa, to shi ne shugabansa har sai ya fita[5]”.

Daga Ja’afar bn Muhammad daga babansa (a.s) ya ce: “Idan wani daga cikinku ya shiga wajen dan’uwansa, to ya zauna a inda mai gidan ya umarce shi da zama, saboda mai gida shi ya fi sanin sirrin gidan sama da wanda ya shigo[6]”.

YanayinZama

d) – Yanayin zama, Sayyid Abdul’azim al-Hasani yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya kasance yana zama yanayi uku: ya kan mike kwabrinsa ya tarbe su da hannayensa, ya dora hannunsa a zira’insa, ya kasance ya kan durkusa a kan gwuiwoyinsa, kuma ya kan nade kafa guda ya shimfida gudar a kan dayar, ba a taba ganinsa (s.a.w.a) ya mike kafa yayin zama ba[7]”.



1 2 3 4 5 6 7 8 next