Kabarin manzo



4-Allama Amini tare da tare da bin diddiki wanda ya ci a yaba masa, ya tattara ruwayoyi da dama akan ziayarar manzo s.a.w.a.saboda haka anan kawai zamu yi nuni da daya daga cikin ruwayoyi da ya samo daga littafi 41 da a ka ruwaito a kan hakan.Al-Gadir

 Saboda haka kawo dukkan ruwayoyin da danganensu ba zai yiwu ba a nan,saboda haka kawai anan zamu takaita ne da kawo wasu kawai daga cikinsu.Wadan da suke son Karin bayani sai su koma zuwa littafin da aka ambata a sama.

 Hadisi na farko:"Wanda duk ya ziyarci kabarina aljanna ta wajaba a garesa"Darul kutni assunan:2:278 babin al-mawakit hadisi na 194,Al-ahkamul suldaniyya:150.wannan hadisi Allama Amini ya ruwaitosa tare da dangane daga littafi 41.

Hadisi na biyu:Dabarani a cikin mu'ujamul Kabir,Gazali a cikin ihya'u ulum daga Abdullahi bn umar,Manzo yana cewa:"Duk wanda yazo ziyara kuma saboda kawai ziyarata ya zo,to ya wajaba in cece shi a ranar kiya."

Hadisi na uku:Darul kutni ya ruwaito  daga Abdullahi bn  umar cewa manzo s.a.w.a. ya ce:Duk wanda ya ziyarce ni bayan wafatina alokacin aikn hajji, to kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye."

Hadisi na hudu:Darul kutni ya ruwaito daga bn Umar cewa manzo s.a.w.a. ya ce:"Duk wanda ya ziyarci kabarina kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye."

 Anan ya kamata mu yi nazarin matsayin ziyara a wajen Aimmatu Ahlul-bait a.s.:

Ziyar manzo a ruwayar Ahlul-bait a.s:

1-Imam Bakir a.s. yana cewa manzo s.a.w.a. yana cewa: "Duk wanda ya ziyarce ni ina raye ko bayan na yi wafati zan kasance mai cetonsa a ranar kiyama"Hamiri:Kurbul asnad:31,Majalisi Bihar:97,139.

2-Imam Ali a.s yana cewa:" ku cika hajjinku da manzon Allah a lokacin da kuka fito daga dakin Allah,domin kin ziyararsa rishin girmamawa ne gare sa,an umurce ku da yin hakan.Tare da ziyarar kaburburan da aka umurce  ku zaku karashe hajjinku."



back 1 2 3 4 5 next