Kabarin manzo



Ziyarar Kabarin Manzo a mahangar Kur'ani da sunna:

A: A mahangar kur'ani mai girma:

Kur'ani maigirma yana bai wa al'ummar musulmi umurni  da su je wajen manzo su nemi gafararsa sannan su nemi manzo s.a.w.a. don ya nema musu gafarar Allah madaukaki:"Duk lokacin da suka zalunci kawunansu (zunubi)idan suka zo wajen manzo suka nemi gafa kuma Manzon ya nema musu gafar a wajen Allah, lallai Allah mai rahama ne kuma mai karbar tuba."Nisaa:64.

 A wani wurin  ciki kur'ani Allah madaukaki yana zargin munafukai da cewa duk lokacin da aka neme su da su je wajen ma'aiki don ya nema musu gafara sai su kiya:"Idan a ka ce musu ko zo manzo ya nema muku gafara, sai  su juya fusakunsu (don  nuna rishin amincewa)zaka ga suna kin maganarka suna masu nuna girman kai."Munafikun:5.

Shehin malamin nan kuma Ahlus sunna, Takiyyud deen Subki,Ya yi imani da cewa:Msuslmi a wannan lokacin ma tare da amfani da wannan aya suna iya zuwa wajen manzo su  nemi gafararsa kuma Allah ya gafarta musu.Ya kara da cewa duk da yake wannan aya ta shafi lokacin da manzo yake a raye ne,amma neman gafara   ta hanyarsa bai kebanta da lokacin da yake a raye ba.Saboda wannan wani mtsayi ne wanda aka bai wa manzo s.a.w.a.don haka sakamakon rabuwarsa da duniya wannan matsayi ba zai kau ba.

Mai yiwuwa a ce:Wannan abin da ya zo a cikin wannan aya  da muka ambata a sama, ya kunshi nuna matsayi da daukaka ta manzo ne kawai,amma aiwatar da wannan ya kebanci lokacin rayuwarsa ne kawai,amma ba lokacin da baya duniya ba,ta yadda alakarmu da shi ta yanke.

 Amma wannan magana sam ba abin karba ba ce,domin kuwa dalilan da za mu ambata a nan gaba suna bayyana cewa rasuwar manzo sam ba ta da wani tasiri akan wannan al'amari,don haka mutuwa da rayuwarsa babu wani bambanci duk daya ne:

1-Mutuwa ba tana nuna karshen dan Adam ba ne,mutuwa wata sabuwar kofa ce don  shiga wata sabuwar rayuwa kuma duniyar da duk abin da yake a ckinta ya fi abin da yake a duniyar da ta gabata ga rauywar  dan Adam,saboda haka mutum rayayye ne a waccan duniya yana gani kuma yana ji.Musamman shahidai wadan da bayan sun dandana shahada zasu cigaba da karbar ci da sha daga Allah madauakin sarki,kuma suna cikin jin dadi na musaman ta hanyar ruhinsu.Saboda haka zamu yi bayani akan wannan anan gaba a cikin bahasin rayuwar barzahu.Ali Imraan:169'179'Bakara:154,Yasin:27,27 da sauran wurare.

2-Ya zo da yawa a cikin ruwaya cewa: salatin da  musulmi suke yi wa manzo akwai mala'iku na musamman masu isar da wannan salati zuwa ga manzo s.a.w.a.don haka duk inda mutum yake idan ya yi wa manzo salati zai isa zuwa ga manzon. Kamar yadda yake cewa:"Ku yi mani salati,salatin yana isa zuwa gare ni  daga duk inda kuke"Taji Jami'u lil'usul:2/179.

3-Musulmi a wajen tahiyar salla an umurce su da su yi wa manzo sallama,sannan su yi masa gaisuwa, "Assalamu alaika ayyuhan   nabiyu warahamatullahi wa barakatuhu"Wannan gaisuwa ba wai kawai an umurci musulmi ba ne da su yi ta zuwa gamanzo amma shi ba ya jin abin da suke yi,Manzo yana raye kuma yana sauraren mu lokacin da muke yi masa salati.

 Wadan nan abubuwan da muka fada a sama suna nuna cewa Manzo yana raye a rayuwar barzahu,sannan yana da alaka da mu kuma yana jin abin da muke yi.Sannan yana jin rokonmu kuma yana biya mana bukatunmu a lokacin da ya dace.Saboda haka a nan ya kamata mu ce wadan nan ayoyi da muka yi bayani a sama, Suna da ma'ana mai fadi,saboda haka yanzu ma suna kiranmu da ziyarar manzo a kabarinsa kuma mu nemi gafara kuma ya nema mana gafara ga Allah,sannan mu nemi bukatunmu daga garesa.Saboda haka ya zo  a cikin ziyarar manzo da ake karantawa a haraminsa cewa mai ziyara ya nemi gafarar Allah ta hanyar manzon tare da kula da ma'anar ayar da muka yi bayani a sama.Saboda haka ziyarar manzo ba wani abu ba ne sai kawai yin salati ga manzo da kuma neman bukatu da gafarar Allah ta hanyar mazon.Saboda haka wadanan ayoyi na sama suna iya zama sheda akan inganci da mustahabbacin ziyayarar mazo s.a.w.a.



1 2 3 4 5 next