Halayen Imam Hasan (a.s)



Amma kuwa Hunsa shi ne wanda ba a sani ba namiji ne ko mace, don haka sai a saurara idan ya yi mafarki to namiji ne, idan kuwa mace ce to zai yi haila kuma nononsa ya fito, idan ba a samu wadannan ba, sai a gaya masa ya mike tsaye ya yi fitsari, idan fitsarin ya samu bango to namiji ne, idan kuwa fitsarinsa ya yi kasa kamar yadda na rakumi yake yin kasa to shi mace ne.

Amma abubuwa goma da wani ya fi wani karfi su ne; mafi karfin abin da Allah ya halitta shi ne dutse, shi kuwa karfe da yake yanka dutse ya fi shi karfi, abin da kuwa ya fi karfe tsanani ita ce wuta da take narka karfe, ruwa kuwa ya fi wuta tsanani, gajimare ya fi ruwa tsanani, iska kuwa da take daukar gajimare ta fi shi karfi, mala'ikan da yake kora ita iskar ya fi ta karfi, shi kuwa wannan mala'ikan mal'ikan mutuwa da yake dauke ransa ya fi shi karfi, shi kuwa mala'ikan mutuwa mutuwar da take dauke ransa ta fi shi karfi, ita kuwa mutuwa abin da ya fi ta karfi shi ne umarnin Allah da yake ije (ture da tunkude ko ingije) mutuwar.

Imam Hasan (a.s) ya shahara da kyautata wa wanda ya munana masa. Ana ruwaitowa wata rana ya samu wata akuya da aka karya mata kafa sai ya ce: Waye ya karya ta? Sai wani bawansa ya ce: Ni ne. Sai Imam Hasan (a.s) ya ce: Saboda me? Sai ya ce: Domin in sanya maka bakin ciki da damuwa.

Sai Imam Hasan (a.s) ya yi murmushi ya ce: Ni kuwa sai na faranta maka rai, sai ya 'yanta shi, sannan ya ba shi kyauta mai yawa.

Ya kasance mafi bautar mutane ga Allah a zamaninsa kuma mafi iliminsu kuma mafificinsu, kuma ya fi kowa kama da Annabi (s.a.w), kuma mafi girman Ahlul Baiti a zamanisa kuma mafi hakurin mutane.

Ya kasance daga cikin karamcinsa, daya daga cikin kuyanginsa ta mika masa wani damki na turaren kamshi sai ya ce: ke 'yantacciya ce. Sai ya ce: haka nan Ubangijinmu ya tarbiyyantar da mu yayin da ya ce: "Idan aka gaishe da ku to ku amsa da mafi kyawu daga gareta ko kuma ku yi raddinta"[1].

Yana daga cikin hakurinsa cewa wani mutumin Sham ya gan shi yana haye da dabba, sai ya rika la'antarsa shi kuma Imam Hasan (a.s) ba ya yi masa raddi, yayin da ya gama sai Imam Hasan (a.s) ya zo wajensa ya yi masa sallama ya yi dariya ya ce: ya kai wannan tsoho ina tsammanin kai bako ne a wannan gari, ta yiwu ka yi batan kai, amma da ka… roke mu da mun ba ka, da kuma ka nemi shiryarwar mu da mun shiryar da kai, da ka nemi mu hau da kai da mun ba ka abin hawa, idan kuwa kana jin yunwa ne to sai mu ciyar da kai, idan kuwa kana da tsaraici ne to sai mu tufatar da kai idan kuma kana da talauci ne sai mu wadata ka, idan ka kasance korare ne sai mu ba ka wajen zama, idan kuwa kana da wata bukata ne sai mu biya maka[2].

Yayin da mutumin nan ya ji wannan magana sai ya yi kuka ya ce: na shaida kai ne halifan Allah a bayan kasa, Allah ne kawai ya san inda yake sanya sakonsa.

Imam Hasan (a.s) ya yi sulhu da Mu'awiya domin maslahar musulunci da al'umma gaba daya, ba don wannan sulhun ba to da an kashe duk wani mumini wanda ya rage hada da Imam Hasan da Imam Husain (a.s) da sauran alayen manzon Allah da sahabbai da suka rage masu daraja daga cikinsu.

Hukuma a wurin ahlul-bati (a.s) ba wani abu ne ba sai wasila ce ta samun dammar zartar da hukuncin Allah da tsayar da adalci da yada shiriya, amma idan ta kasance sakamakon nemanta zai kai ga kashe mutane ne kawai don haka ne jagoran ahlul-bait (a.s) Imam Hasan (a.s) ya ga ya dace ya bar wannan lamarin domin maslahar da ta fi dacewa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 next