Halayen Imam Hasan (a.s)



Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da bayanin halayen Imam Hasan al-Mujtaba (a.s) da rayuwarsa.

Iyalan gidan manzon Allah (s.a.w) wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya.

Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da yake kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba.

Imam Hasan (a.s) ya kasance madogara a zamaninsa ga dukkan wani mai neman mafaka domin sanin shiriyar da kakansa annabin Allah (s.a.w) ya zo da ita, ya amsa shubuhohin masu addinai da masu neman kawo rudu domin tseratar da al’umma da sharrin batansu.

Imam Hasan (a.s) ya amsa wa sarkin mas'alolin da ya kawo zuwa ga babansa Imam Ali (a.s) domin a amsa masa su, sai Imam Ali (a.s) ya nemi dan sakon ya zabi wani daga 'ya'yansa domin ya amsa masa, sai ya zabi Imam Hasan (a.s).

Akwai wani abu na karama da ya faru yayin da dan sakon ya zo, domin ya gaya wa Imam Ali (a.s) cewa shi daga al'ummarsa yake, sai ya nuna masa cewa karya yake yi, shi yana cikin mabiya Mu'awiya ne, sai mutum ya gaskata hakan sannan sai ya ce; Mu'awiya ne ya aiko shi ya tambayi wannan tambayoyin da sarikin Ruma ya aiko masa shi kuwa ba zai iya amsawa ba.

Daga amsoshin da Imam Hasan (a.s) ya bayar sun hada da cewa:

Tsakanin gaskiya da karya 'yan yatsu hudu ne, domin gaskiya shi ne abin da ka gani, karya kuwa shi ne abin da ka ji. Amma abin da yake tsakanin sama da kasa ita ce addu'ar wanda aka zalunta, da iyakacin abin da gani ya hango. Amma tafiyar wuni daya ita ce abin da yake tsakanin gabas da yamma.  Amma Kausu Kazahin, shi Kazahu sunan shedan ne, shi Kausu sunan Allah ne, kuma shi alama ce ta yalwa da aminci ga mutanen duniya daga dulmiya cikin ruwa.   



1 2 3 4 5 6 7 8 next