Mutum Mai Kamala



Wannan yana nuna mana irin yadda siffofin annabi suka zama sanannu a wannan yankuna ta yadda har yaruntarsa ba ta iya dusashe wannan siffofin ba da masu bauta a dazuka da tsaunuka irin su Bahira suka iya gano shi tun yana karami. Kuma wannan yana nuna tsananin kishirwa da sanin zuwansa da yake tattare da jama’ar wannan zamanin musamman Yahudawa da Kiristoci da larabawan wadannan yankunan.


 

Wahayi

Wahayi a ma’anarsa ta isdilahi yana nufin abin da ake yi wa annabawa da manzanni sakonsa na daga zance ko ilhami da ake kimsa musu (A.S). Kuma shi hanya ce da Allah yake sanar da mutum ubangijinsa da kansa da shiriyarsa domin ya tsara rayuwarsa da zamantakewarsa da sauran halittu, da kuma yadda zai fuskanci ubangijinsa.

Nau’o’in wahayi

1.     Ta hanyar sauti da annabi yakan ji

2.     Ta hanyar mala’ika da yake jiyar da shi

3.     Ta hanyar jefawa ga annabi a cikin ransa

4.     Ta hanyar mafarki

Wahayi Ga Manzon Rahama (S.A.W)

Allah madaukakin sarki ya shirya annabinsa kuma ya tarbiyyantar da shi da tarbiyya mai kyau, ba domin komai ba sai domin saninsa da nauyin da zai dora masa na shiryar da dan Adam da tseratar da shi zuwa ga tafarki madaidaici, ya kasance farkon nau’in wahayin da ya fara ga manzon rahama shi ne ta hanyar mafarki na gari[8].

Daga cikin hanyoyin tarbiyyantarwa ga annabi da ubangijinsa ya shirya masa sun hada da;

a.      Ilhama da mafarkin gaske da yake nuna masa zahirin abin da yake faruwa a gaske



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 next