Mutum Mai KamalaCikakken Mutum Mai Kamala

Hafiz Muhammad Sa’id

hfaza@yahoo.com

Kuma lalle hakika kana da ladar da ba ta yankewa. Kuma lalle hakika kana kan halayen kirki manya[1].

Shimfida

Daga Allah ne muke neman taimako muna gode masa a cikin kowane hali muke na farin ciki da bakin ciki, kuma muna gode masa a kan rahamarsa da sakon da ya aiko annabawa da shi, musamman annabin karshe Muhammad (S.A.W) Dan Abdullah (A.S) Dan Abdulmudallib (A.S) tsira da amincin Allah su tabbata ga alayensa tsarkaka. Wanda shi ne aka aiko da kur’ani domin ya fitar da mu daga duhu zuwa haske, ya tseratar da mu daga bata, ya canja mana mafi munin al’adu da shiriya zuwa tafarki madaidaici. Sai muka bi shi muna masu mika wuya, muka yi koyi da shi, ya zama mana abin koyi kyakkyawa.

Saudayawa idan marubuta zasu yi rubutu game da tarihin rayuwar wani mutun sananne mai daraja da muhimmanci a tarihin rayuwar dan Adam, sukan fifita bincike game da bangaren rayuwarsa ta ilimi da kyawawan dabi’unsa daidai gwargwadon bukatun su da suke hankoron cim musu ta hanyar bincike game da wannan mutum, sai dai mu a wannan makala zamu yi bincike game da sirar mafi girman mutum, mafificin halitta, mafi tsarkin samammu, shi ne cikamakoin annabawa da manzanni da Kur’ani ya siffanta shi da cewa:

“Ba ya magana da son rai, sai dai shi wahayi ne da aka yi masa shi”.

Da fadinsa: “Ba mu aiko ka ba sai rahama ga talikai”.

Ya umarce mu da mu rike shi abin koyi, yana mai fadin: “Lallai kuna da abin koyi kyakkyawa ga manzo”.

Manufar da ake son kai wa gareta ita ce; sanin annabi Muhammad (S.A.W) domin mu dauki darussa da abin la’akari mu kuma yi koyi da shi, mu lizimci abin da ya zo da shi da umarni, mu koyi sadaukarwa saboda muusulunci daga gareshi, kuma kada mu yi gezau ko rauni gaban abubuwa masu rudarwa, sai ya zama mana alami kuma jagora mafi daukaka a wannan rayuwa.

Zamu yi kokarin yin bincike game da sirar annabi (S.A.W) da suka hada da bincike game da sanin annabi (S.A.W) da haihuwarsa, da tijararsa, da bishararsa, da annabta, da matansa, da wahayin manzanci, da kira a boye da fili, da hijirar annabi, da yakokinsa, zuwa bude Makka da hajjin bankwana, da halifan annabi (S.A.W) zuwa wafatinsa.

Muna rokon Allah ya sanya mu daga wadanda saka kari musulmi wajan sanin wani abu daga tarihin annabinmu, domin ya zama mana haske kuma ya karbi wannan dan kadan daga ayyukanmu ya yi mana gafara, domin shi ne mai karbar tuban muminai. Kuma ina rokonsa ya bayar da ladan ga wanda aka rubuta makalar game da shi (S.A.W) musamman da aka ambaci wannan shekarar da sunansa. Kuma muna rokon Allah madaukaki ya hada kan musulmi gaba daya musamman da gabatowar makon hadin kai.

Hafiz Muhammad Sa'id Kano Nigeria

hfazah@yahoo.com1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 next