Tarihin Fatima Zahra [a.s]



(13) An ruwaito daga Manzon Allah yana cewa, Allah Mabuwayi da daukaka ya halicce ni da Aliyu, Fatima, Hasan. Husaini daga haske guda daya.

(14) An ruwaito daga Manzon Allah yana cewa farkon wacce za ta fara shiga Aljanna ita ce Fatima binti Muhammad.

An ruwaito daga Ummu Salama tana cewa Fatima binti Muhammad ta fi kowa kama da Manzon Allah.

An ruwaito daga A'isha tana cewa: Ban taba ganin wanda ya fi Fatima gaskiyar zance ba in banda Mahaifinta.

An ruwaito daga A'isha tana cewa: Ban taba ganin wanda ya yi kama da Manzon Allah wajen kawaici. kauna. tafiya. tsayuwa, zama. shiriya, kamar Fatima ba.

An ruwaito daga Imam Aliyu (as) yana cewa: Wata rana na tambayi Manzon Allah da ni da Faima wannene ya fi soyuwa gare ka? Sai ya ce kai ka fi ta jarunta gurina. amma ita ta fi soyuwa a gare ni.

An ruwaito daga Manzon Allah (saw) yana cewa: Idan kiyatna ta tsaya. mai yekuwa zai yi yekuwa daga karkashin kaFarshi yana cewa: Ya ku taron jama a ku runtse idanunku har sai Fatima ta ketare siradi. An ruwaito daga Manzon Allah (saw) yana cewa Fatima lta ce mafi alherin matan Aljanna.

An ruwaito daga Abi Abdullahi (as) yana cewa Fatima tana da sunaye tara a wajen Allah mabuwayi da daukaka: Fatima, Siddika, Mubaraka. Dahira. Zakiyya. kadiyya. Mardiyya. Azzahra. Muhaddisa. don Allah ya yay c ta daga dukkan sharri Ba don Aliyu (as) ba da babu wanda ya lsa ya aure ta. mutum ne ko waninsa. Imam Shafi’i yana cewa cikin wake: lyalan gidan Manzo sune marikana Gare su na riki wasilata Da su nake fata ran kiyima A ban takarda ta a hannun dama

Mai karatu babu wani alkalami na mutum ko Aljani wanda zai iya zuwa maka da duk falalar Nana Fatima (as). A duk lokacin da mutum yaji ya tuke gun falalar Fatima (as). a lokacin ne ya sa dan ba. Don haka mun dan zo ne da kadan daga cikin abin da Malaman sunni da shi'a suka rubuta cikin littattafansu Ya Allah sanya mu cikin ceton Fatima (as) amin.Ga wasu wakokin Alhaji

MUSTAPHA GADON KAYA NA BATULA:-

1.  Asalin Zahara'u hasken Allah ne da akwai dalili, Allahu Nurussamawati ga dan misali.
Muhammadu gudan fitilar haske da Imamu Ali, Hasken da ya haskake komai shi ne Batula.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next