Tarihin Fatima Zahra [a.s]



 Ko matan Mahaifinki sun san Fatima ke ce kan gaba.

 Laisa kamisliha duk duniya ba a yo tamkar ki ba.

 Ba ai ba ba kuma za a yi wata wadda ta kai darajarki ba.

7. Domin dukka mu'ujizar da aka ba Manzo ba wanda ba a ba ta ba.

Tana lafih a dutse yana gaishe ta yana mata marhaba.

Kai har bishiya in ta hango Zahra tanai mata ladubba.

 Wace ce mai daraja ake mata wannan in ba Azzahrau ba?

8. Aljanna kece mabudinta diyar Manzona Mujtaba.

Da ba don makiyanki ba Allah-ba zai yi Jahimu ba.

In banda ke ban ga wanda Allah yake fushi da fushinta ba. Yakan kuma yarda in kin aminta don haka ban ga tamkar ki ba. 9. Kaunar Zahra"u wajibi ne. a gare ta za ka san rahma. In alfarma kake nema kai Malam zo ka bi Fatima. Domin ita ce mai rabon Jannatul Firdausi ita Fatima. Mai son ta ya rabauta. makiyanta sam ba za su rabauta ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next