Tarihin Fatima Zahra [a.s]TARIHIN FATIMA ZAHRA [A.S]

MARUBUCI: ABUBAKAR ABDULLHI KADUNA

DARAJOJIN NANA FATIMA (as)

(1). An ruwaito daga Manzon Allah (saw) yana ce wa Fatima (as): "Ya diyata Allah ya yi dubi ya zuwa mazajen duniya sai ya zabe ni daga cikinsu. Sannan ya yi dubi na biyu sai ya zabi mijinki. Sannan ya yi dubi na uku sai ya zabe ki Shugabar matan duniya baki daya. Sannan ya yi dubi na hudu. sai ya zabi 'ya'yanki a kan Shugabannin samari baki daya." (2). An ruwaito daga Baban Ja'afar. Baqir (as) cewa an tambaye shi: "Don me aka ambaci Fatima (as) da suna Zahra9" Sai ya ce: "Domin Allah (swt) ya halicce ta ne da hasken Azma dinsa. Lokacin da Allah (swt) ya halicce ta sai haskenta ya haskake sammai. kassai da fuskokin Malaiku. sai suka fadi suna masu sujuda. Suna cewa ya Ubagijinmu. abin bautanmu wannan wane haske ne' Sai ya yi musu wahayi yana cewa: wannan haske ne daga haskena Na halicce shi ne daga Azmata. Zan sanya shi yana fita daga gadon bayan wani Annabi zuwa gadon bayan wani Annabi. har sai na fitar da shugabanm (A'imma) wadanda za su dinga shinar da mutane a kan hanyata bayan yankewar wahayi "' (3) An ruwaito daga Ibn Abbas yana cewa: 'Wata rana Manzo yana zaunc. a tare da shi akwai Aliyu. Fatima. Hasan da Husaini. sai ya ce: ' Ya Ubangiji ka sani wadannan su ne iyalan gidana mafidarajar mutanc a gurina. Ka so duk mai son su. ka ki duk mai kin su. kajibinci al'amann duk wanda ya goya musu baya. ka yi gaba da duk wanda ya  cigaba da su. ka taimaki duk wa'nda ya taimaka musa. ka tsarkake su daga dukkan najasa. ka kangc su daga dukkan sabo. ka taimake su da Ruhi mai tsarki (Ruhul kudus)'

Sannan sai ya ce: ' Ya Aliyu kai ne Shugaban al"ummata. kai ne Khalifana bayan ba ni. kai ne za ka jagoranci muminai ya zuwa Aljanna Yanzu ina ganin kamar ga diyata Fatima ta taho za ta shiga Aljanna ranar tashin knama cikin haskc. A dama da lla akwai Malaiku dubu saba in (70.000). a hagu da lta akwai Mala'iku dubu saba in. gaba gare ta akwai Mala'iku dubu saba'in. baya gare ta akwai Mala'iku dubu saba' in. Ta Jagoranci mata muminai zuwa Aljanna. Duk matar da ta yi salloli biyar. ta yi azumin watan Ramadan. ta yi hajji (in ta samu iko), ta yi zakkar dukiyanta {in tana da shi}Ta yi wa mijinta biyayya{a kan da' a}

sannan ta mika wa Aliyu walicci bayana. za ta shiga Aljanna da ceton diyata Fatima. Lallai ita ce Shugabar matan duniya.'

Sai wani ya ce: ' Ya Manzon Allah Shugabar matan duniya na zamaninta?" Sai Manzo ya ce 'Wannan ita' ce Maryam binti Imran. Amma diyata Fatima ita ce Shugabarsu tun daga na farkonsu har zuwa na karshensu. Idan ta mike za ta yi salla Malaiku makusanta (mukarrabin dubu saba'in ne suke saukowa su yi mata sallama. sannan su yi yekuwa kamar yadda suke yi wa Maryam, suna cewa " Ya Fatima Allah ya zabe ki ya tsarkake ki. sarman ya fifita ki a kan sauran matan duniya baki daya.

Sannan sai ya juyo gun Aliyu (as) sai ya ce. "Ya Aliyu. lallai Fatima tsoka ce daga gare ni. ita ce hasken idona. ita ce furran zuciyata Yana bakanta min duk abin da ya bakanta mata. yana faranta min duk abin da ya faranta mata. Ita ce farkon wanda zai nske ni cikin iyalan gidana. bayan wafatina. don haka ka kyautata mata bayana."

"'Sannan Hasan da Husaini ‘ya’yana ne*. ababen begena. su ne shugabannin samarin Aljanna. Su zamo kullum cikin kulawarka. Sannan sai ya daga hannuwansa sama yana cewa: ' Ya Ubangiji ina shaida maka cewa in masoyin masoyinsu ne. kuma makiyin makiyinsu ne. mai aminci ga duk wanda ya amince musu. sannan mai daura damaran yaki ga duk wanda ya yake su!!!"

(4). An ruwaito daga Fatima Azzahra binti Rasulullah tana cewa: "Wata rana mahaifina ya shigo gidana sai ya yi min sallama. sai na amsa masa Sai ya ce 'Ni ina jin zazzabi." Sai na ce Allah ya yi maka tsari da zazzabi ya Babana. Sai ya ce Ya Fatima ki lullube ni da bargo sakar Yamani Sai na dauko bargon na lullube shi. ina kallon fuskarsa tana hasko kamar farin wata daren goma sha biyu. Can an jima sai ga dana Hasan ya shigo ya yi sallama. na amsa da cewa Wa'alaikas salam ya hasken idona. tarin cikin zuciyata. Sai ya ce 'Ina jin kamshi mai dadi kamar na kakana Manzon Allah (saw ).' Sai na ce na'am ya dana. kakanka ne kwance cikin bargo ba shi da da lafiya. Sai Hasan ya nufi gun da Manzo yake. Sai ya ce Assalamu alaika ya Kakana. Assalamu alaika ya Manzon Allah. ka yi min izini in shigo tare da kai." Sai Manzo ya amsa masa. yana mai cewa"Na maka izini ya dana. ma'abocin tafkina Alkausar.

"Ba a jima sosai ba sai ga dana Husain ya shigo sai ya yi sallama. sai na amsa mishi. ina mai cewa wa alaikassalam ya hasken idona farin cikin zuciyata. Sai ya ce , ina jin kamshin mai dadi kamar na kakana

Manzon Allah.' Sai na ce na'am, Kakanka ne da dan’uwanka cikin mayafi Sai ya nufi gurin dasuke. Sai yace 'Assalamu alaika ya Kakana, Assalamu alaika ya wanda Allahya zaba, ka yi min izini in kasance tare da ku.' Sai Manzo yaamsa masa yana mai cewa 'Na maka izini ya dana, mai ceton al'ummata.' Sai ya shiga tare da su.1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next