Alamomin Soyayya



Alamomin (Natijoji) Soyayya

Hujjatul Islam Muhammad Raishahari

Hafiz Muhammad Sa’id Kano

9 / 1

Alamomin Gaskiyar Soyayya

A- Shaidawar Zuci

323. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ku tambayi zukata game da soyayya, domin ita shaida ce da ba ta karbar rashawa[1].

324. Littafin Kafi, daga salihu dan hakam: na ji wani mutum yana tambayar Abu Abdullahi (A.S) sai ya ce: mutumin da ya ce idan kaunarka, yaya zan san yana sona? Sai ya ce: ka jarrabi zuciyarka, idan ka kasance kana sonsa to shi ma yana sonka[2].

325. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: ka duba zuciyarka, idan ta ki abokinka, to hakika dayanku ya yi wani abu[3].

326. Daga littafin Uyunu akhbarir Ridha (A.S), daga Hasan dan Jaham: na tambayi Ridha (A.S) sai na ce masa: Ina fansarka da raina, ina son in san yaya nake gunka? Sai ya ce: Duba ka gani yaya kake guna[4].

B- Taimakawa A Boye Da Sarari

327. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi gaskiyar ‘yan’uwa a soyayya shi ne wanda ya fi su taimako ga ‘yan’uwansa a cikin sauki da tsanani[5].

328. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: a cikin kunci da tsanani ne kyakkyawar kauna take bayyana[6].

C- Ambaton Masoyi

329. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: wanda ya so abu zai yawaita ambatonsa[7].

D- Barin Dadin Baki

330. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Hakika wanda yake sonka shi ne wanda ba ya yi maka dadin baki, kuma wanda yake yabonka shi ne wanda ba ya jiyar da kai (yabon)[8].



1 2 3 4 next