Hakkokin Soyayya



319. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: ku ba wa ‘yan’uwanku uzuri a kurakuransu da kuma zamiyar nan ta gajiyawarsu, idan kuma ba ku samu wani uzuri garesu a wannan ba, to ku yarda da cewa wannan takaitawarku ce saboda gajiyawarku na sanin hanyoyin bayar da uzuri[27].

0- Tambayar Wanda Ba Ya Nan

320. Daga littafin makarimul akhlak, daga Anas, daga Manzon Allah (S.A.W) ya kasance idan ya rasa wani mutum daga ‘yan’uwansa kwana uku sai ya tambaya game da shi, idan ba ya nan sai ya yi masa addu’a, idan kuwa yana nan sai ya kai masa ziyara, idan kuwa ba shi da lafiya ne sai ya gaishe da shi[28].

8 / 3

Tattararrun Hakkokin ‘Yan’uwa

321. Daga Imam Zainul Abidin (A.S) ya ce: amma hakkin aboki sai ka yi musharaka da shi a cikin alheri matukar zaka iya hakan, idan kuwa ba haka ba to mafi karanci shi ne ka yi masa adalci. kuma ka girmama shi kamar yadda yake girmama ka, kuma ka kiyaye shi kamar yadda yake kiyaye ka. kuma kada ya riga ka cikin abin da yake akwai girmamawa tsakaninka da shi, idan kuwa ya riga ka sai ka saka masa. kuma kada ka takaita masa abin da ya cancanta na (ka nuna masa na) kauna, ka lizimtawa kanka nasiharsa, da kiyaye shi, da kuma taimaka masa a kan biyayyar ubagijinsa, da kuma taimakon sa a kanka cikin abin da ba a nufin sabon Ubangijinsa da shi, sannan kuma ka kasance tausayi (rahama) gareshi, kada kuma ka kasance azaba a kansa[29].

322. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Abota ba ta kasancewa sai da iyakokinta, duk wanda yake da wadannan iyakoki ko wani daga cikinta, to ka danganta shi zuwa ga abota (wato; abokinka ne), wanda kuma ba shi da wani abu daga gareta to kada ka danganta shi da wani abu na abotaka; na farko: badininsa da zahirinsa ya kasance daya ne gareka. Na biyu: ya ga cewa adonka adonsa ne, kuma aibinka aibinsa ne. na uku: kada ka canza masa kauna ko dukiya. Na hudu: kada kuma ya hana ka wani abu da yake da ikonsa. Na biyar: -ya hada duk abin da aka fada- kada ya mika ka (ya bar ka) gun wahalhalu[30].


[1] Gurarul hikam: 2686.

[2] Gurarul hikam: 7157.

[3] Gurarul hikam: 3017.

[4] Alkafi: 8, 162, 166.

[5] Tafsirul kummi: 1, 172.



back 1 2 3 4 5 6 next