Hakkokin SoyayyaHakkokin Soyayya
Hujjatul Islam Muhammad Raishahari
Hafiz Muhammad Sa’id Kano 8 / 1 Himmantuwa Da Hakkokin ‘Yan’uwa
293. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: a cikin wasiyyarsa ga dansa Muhammad dan hanafiyya: ya kai dana… kada ka tozarta hakkin dan’uwanka haka nan kawai kana mai dogara da alakar da take tsakaninka da shi; ka sani wanda ka tozarta hakkinsa ba dan’uwanka ba ne[1]. 294. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka kasance mai kiyayewa ga so, koda ba ka sami mai kiyaye wa ba[2]. 295. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi kyawun mutunci shi ne kiyaye soyayya[3]. 296. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Allah madaukaki yana kiyaye wa ga mai kiyaye abokinsa[4]. 8 / 2 Hakkokin ‘Yan’uwa
a- alfarmar rai da dukiya 297. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ku saurara ya ku mutane, hakika musulmi dan’uwan musulmi ne da gaskiya[5]. b- Mayar Da Gaisuwa
298. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: hakika musulmi dan’uwan musulmi ne idan ya hadu da shi sai ya mayar masa da sallama kwatankwacin yadda ya yi masa ko mafi kyawu daga hakan[6].
|