Shimfida Da Gabatarwa



·        Wasu suce: Hanin yazo ne a lokacin shekarar Budi (Amul-Fat-hi) .

·        Wasu suce: Ta kasance anayi, sai dai an hana ta ne a Yakin Tabuka.

·        Wasu suce: anyi umarnin yinta lokacin Hajjin Ban-kwana (Hajjatul-wada' i), sannan daga baya aka hana.

·        Wasu suce: An halasta sannan aka haramta, aka sake halastawa aka haramta, aka halasta aka haramta.

·        Wasu kuma suka fadi sabanin haka. (Ahkamul-Kur' an: 2/184-195, Babul-Mut'ati. Sahihul-Muslim Sharhin Nawawiy: 9/179, Babu Nikahul-Mut' ati. Irshadus-Sari abisa sharhin Sahihul-Bukhari: Babi na 32,"Babi naha Rasulullahi (Sallallahu alaiHi wa Alihi) an Nikahul-Mut' ati, Hadisai na; 5115, 5119.

Hujja wacce take yankakkiya tana tabbatar da rashin shafe hukuncin auren Mutu'a ne, wanda mafi karfin wadannan dalilai shine kokonto da yawan sabanin magana kan shafewar. Har ta kai ga Malam Muslim cikin littafinsa na Hadisi Babin Mutu'a, da "Babu Nikahul-Mut' ati" ya bayyana cewar an halasta sannan aka shafe, aka kuma halastawa aka shafe, aka sake halastawa aka kuma shafewa, sannan yace an haramta shi har zuwa Alkiyama. (Sahih Muslim: 2/130). Kai kaji sai kace a cikin wani Wasan kwaikwayo.

Malam Kurdabi ya ruwaito cikin Tafsirinsa abinda Ibnul-Arabi ya fada na cewar: Ita shafewar ta dauki wannan hukuncin sau biyu ne, sannan yayi karin bayani akai da fadinsa. Wanin sa kuwa daga cikin wadanda suka hada hadisai daban-daban, yace: "Hakika tana kira kan halasci da haramci har sau bakwai" sannan ya harhada maganganun shafewar yace: "Wadannan sune maganganu guda bakwai da aka halasta Mutu'a sannan aka haramta" (Tafsirin Kurdabi: 5/130 – 131).

Shin wannan wane irin Addini ne wanda bashi da cikakkiyar alkibla, yake yawan kwan-gaba-kwan- baya. Irin wannan ne yasa wanda yayi littafin Ayoyin Shaidan "The Satanic Berses" Allah ya tsine masa, ya sami damar ciwa Addinin Musulunci da Annabawa mutunci. Saboda yayi amfani da irin wadannan ruwayoyin ne na ace Annabi Muhammad (Sallallahu alaiHi wa AliHi) yau yace kaza gobe yace kaza, wanda ya saba da wancan. Da ruwayoyin da suke su kansu cin mutunci ne ga Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi). kamar Hadisan da suke cewa: wai Annabi (Sallallahu alaiHi wa AliHi) yana shan "Nabiz" (jikakken Inibi, wanda kuma a matsayin Giya yake don yana bugarwa). Ko kuma irin su Hadisan da ake ruwaitowa wai Manzo (Sallallahu alaiHi wa AliHi) yana Fitsari a tsaye, wal iyazu billa. Wanda shi mutum bazai taba yarda a fadi haka akan Babansa ba. Idan ka duba cikin Sihahus-sitti na Ahlus-Sunna zaka taras da dimbin irin wadannan Hadisai. Wanda mu a Mazhabar Ahlul-Baiti bama yarda da irin wadannan maganganu. Muna dauka dai wani kirene ga Manzo (Sallallahu alaiHi wa AliHi) domin kuwa Ubangiji Madaukakin Sarki yana cewa:

"وما ينطق عن الهوى, إن هو إلا وحي يوحى"  (النجم 3-4)

Ma'ana:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next